https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client=ca-pub-3044793792529166 src='https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client='/> Yadda Za a Inganta Aikin Ƴan Sanda a Najeriya - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Yadda Za a Inganta Aikin Ƴan Sanda a Najeriya

Yadda Za a Inganta Aikin Ƴan Sanda a Najeriya

Yadda Za a Inganta Aikin Ƴan Sanda a Najeriya


A ranar Litinin, 7 ga watan Afrilu, aka gudanar da bikin ranar ƴan sanda a Najeriya – rana da aka ware domin tunawa da gudunmawar da rundunar ke bayarwa da kuma nazarin hanyoyin inganta aikinta da rayuwar jami’anta.


Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya kafa wannan rana, domin ta zama lokaci na tunawa da ƙalubale da nasarorin rundunar, tare da lalubo sabbin dabarun ci gaba.


A bikin da aka yi a Eagles Square, Abuja, mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilci shugaban ƙasa inda ya bayyana kudirin gwamnati na sake fasalin rundunar don dacewa da zamani.


Amma ta yaya ne za a inganta aiki da walwalar ƴan sanda a Najeriya?


Ra’ayoyin Jama’a Game da Ƴan Sanda


Da yawa daga cikin jama’a na kallon ƴan sanda a matsayin masu cin hanci, rashawa da zalunci – kamar yadda wani ɗan sanda da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya shaida wa BBC.


A cewarsa: “Mutane na kallon mu a matsayin masu cin hanci da rashin tausayi. Da ba don rashin aikin yi ba, da matasa ba za su yi sha’awar shiga aikin ɗan sanda ba saboda matsalolin da ke ciki.”


Sai dai Malam Kabiru Adamu, masani kan harkokin tsaro kuma shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence, ya bayyana cewa kallon da ake yi wa ƴan sanda ba laifinsu ba ne gaba ɗaya.


A cewarsa: “Akwai abubuwa masu muhimmanci da idan ba a gyara su ba, aikin ƴan sanda ba zai samu kima ba a idon jama’a.”


Hanyoyin Inganta Aikin Ƴan Sanda


Malam Kabiru ya bayyana cewa muhimmin hanyar inganta aikin ƴan sanda ita ce tabbatar da walwala da jin daɗin jami’an tsaron. Ga wasu muhimman hanyoyi:


Kayan Aiki na Zamani: Ƴan sanda su rika samun motoci, babura, makamai da kayan aiki masu inganci domin sauƙaƙa musu aiki.


Sutura Mai Kyau: Kaya na musamman da ya dace da aiki zai ƙara musu kwarin guiwa da girmamawa daga jama’a.


Albashi da Fansho: Ana buƙatar ƙara albashi da alawus domin gujewa cin hanci da kuma tabbatar da walwala, musamman bayan ritaya.


Kulawa da Lafiya: Jami’an tsaro su samu wuraren kula da lafiya, ko suna cikin aiki ko bayan sun bar aiki.


Muhalli: Gwamnati ta samar da matsuguni masu kyau domin jama’a su iya aiki da natsuwa da kulawa da iyali.



Ƴan Sanda – Su Na Wa Ya Isa Najeriya?


Malam Kabiru ya musanta cewa akwai ƙayyadadden adadin jami’an da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware wa kowace ƙasa. Amma ya bayyana cewa Najeriya na da buƙatar ƙarin jami’an tsaro saboda yawan aikace-aikace da kuma yawan jama’a.


A shekarar 2024, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana aniyarsa na ƙara yawan ƴan sanda da samar musu da kayan aiki domin inganta tsaro da adalci a fadin ƙasar.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel