https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client=ca-pub-3044793792529166 src='https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client='/> Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game da Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game da Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi

Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game da Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi

Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game da Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi


Bayan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi, mutane da dama musamman Musulmai a Najeriya sun cika da alhini da addu'o'in neman rahamar Allah a gare shi. A yayin da ake ci gaba da tunawa da rayuwarsa, ga wasu muhimman abubuwa guda biyar da suka shafi rayuwarsa da ba kowa ya sani ba:



1. Asalin Haihuwa da Rayuwar Farko


An haifi Sheikh Idris a garin Gwaram da ke ƙaramar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi a shekarar 1957. Ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya kafin Allah ya karɓi rayuwarsa, lamarin da ya sa ya yi yawon neman lafiya har zuwa ƙasashen Saudiyya da Indiya. Ya rasu ya bar mahaifiya, mata uku da ƴaƴa guda 32.


2. Ilimi da Ƙwarewa


Sheikh Idris mutum ne da ke da Æ™wazo wajen neman ilimi. Ya samu digiri na farko, na biyu da kuma digiri na uku (PhD) a fannin Shari’ar Musulunci. Ya halarci jami’o’i da dama ciki har da Madina, Sudan, Jos da BUK (Kano). A cewar É—alibinsa Injiniya Ayuba Abdullahi, Sheikh ba ya bata lokaci – tun daga safiya har yamma kullum yana cikin koyarwa ko bincike.


3. Halayya da FaÉ—in Gaskiya


Sheikh Idris mutum ne mai tsantsar gaskiya kuma mai bayyana ra’ayinsa kai tsaye. Idan ya fahimci wata magana ko al’amari, to yana fitar da ra’ayinsa a fili ba tare da É“oyewa ba. Duk da cewa wasu a kafafen sada zumunta na kallonsa da fusata, makusansa sun bayyana cewa malam mutum ne mai sauÆ™in kai kuma ba ya É—aukar zafi ko riÆ™e a rai. Yakan faÉ—i gaskiya, kuma da zarar ya faÉ—i ra’ayinsa, sai ya wuce ba tare da damuwa da baya ba.


4. Sana'a da Taimakon Kai


Ba kamar wasu malamai da suka mayar da wa'azi sana’a ba, Sheikh Idris ya kasance É—an kasuwa ne da ya rungumi noma da harkokin kasuwanci. Yana da makarantu (nazare, firamare da kwaleji) a Bauchi, shagunan kayan masarufi, na magunguna da kuma cibiyoyin kasuwanci. Duk da haka, bai hana shi cigaba da bada ilimi da wa’azi ba.


5. Zumunci da Ayyukan Jinƙai


Sheikh Idris mutum ne mai matuƙar ƙaunar zumunci da ayyukan alheri. Yakan ɗauki iyalansa ya kai su ƙauye don sada zumunta, yana kuma kai musu kyauta. A makarantar sa, akwai marayu da dama da ke karatu kyauta, yana saya musu kayan makaranta da tallafi. Lokacin da matsin tattalin arziki ya yi ƙamari, Sheikh ya sanar da cewa duk ɗaliban sa su ci gaba da karatu ba tare da biyan kuɗi ba.


Rasuwar Malamin da Jana'izarsa


Sheikh Idris ya rasu da misalin Æ™arfe 11 na dare ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi. An gudanar da jana’izarsa a masallacin Idin Games Village da ke Bauchi da misalin Æ™arfe 10 na safiyar Juma’a, inda dubban mutane suka halarta. Kungiyar JIBWIS da sauran malamai da dama sun aika da sakon ta’aziyya da alhini bisa wannan babban rashi.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel