src='https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client='/> Tufafin Annabi Muhammad (SAW) - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Tufafin Annabi Muhammad (SAW)

Tufafin Annabi Muhammad (SAW)

 Tufafin Annabi Muhammad (SAW)


Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance yana zaben mafi kyawun tufafi ba tare da girman kai, ko almubazzaranci ba. Zai zaɓi tufafin da ya fi dacewa da jikinsa, kuma ya sami motsawa cikin sauƙi (ba matsatstsun kaya ba, ba musu girman da ya wuce kima ba), ya na guje wa kaya masu fadi da yawa, ko musu dogon hannayen da suka wuce gabar hannu, da dogayen tufafin da suka wuce idon sawu. Rawaninsa bai yi girma da yawa ba kuma baiyi ƙanƙanta wajen kare zafi ko sanyi ba. Tufafinsa sun bambanta, wani lokaci yana sa na ulu wani lokaci na auduga.


Yana sa tufafi daban-daban, kamar Alkyabba, Izar (ƙananan tufa), Burdah (alkyabba), Khameesah (shirt), da Mirt (rawani). A wasu lokuta, yakan sanya tufafin da aka keɓe kamar riguna da aka dinka, da Qubaa (tufafin da ake sanyawa akan riga). Bai yi riko da wani nau'in tufafi daya kawai ba.


Bayanan sutturarsa sune kamar haka.


Irin Tufafin Annabi Muhammad (SAWW)


Isaba: Wannan yana nufin duk wani abu da ake nade kai. An ambaci cewa a karshen rayuwar Manzon Allah, ya sanya ishaba.


Al-Amama: Wannan sanannen abin rufa kai ne a tsakanin Larabawa, wanda kuma ake kira "Tiǧān al-'Arab" (rawanin Larabawa). Ya zo cikin hadisai da dama. Annabi ya kasance yana sanya shi da shigarsa ta musamman, yana nade shi, ya bar wani sashinsa a kwance a tsakanin kafadunsa. Akwai hanyoyi daban-daban da za a iya sanya rawani, amma ba a iyakance su ga hanya ɗaya kawai ba. Ana iya yin shi daga yadudduka daban-daban, wani lokaci da yadi iri ɗaya kamar tufa. Annabi ya sanya rawani iri-iri, ciki har da baki kamar Harqaniyyah, da Huṭukiyyah, da Qiṭriyyah. An bayyana cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya shiga Makka ne a ranar da aka budeta yana sanye da bakin rawani.


Izar: Wannan kalma tana nufin duk wani abu da ya lullube mutum, kuma ana amfani da shi musamman wajen siffanta tufa da ke rufe kasan jiki, tana boye al'aura. Ba a yi shi da wani takamaiman yadi ba. Izar ya zo a cikin hadisai da dama, kamar fadin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: “Abin da yake kasa da idon sawu yana cikin Wuta”. An taba gayawa Sahabbai cewa Annabi zai fito zuwa gare su sanye da izar. A farkon zamanin musulunci, kalmar izar tana nufin tufa ne kawai, daga baya kuma, ta ke yin nuni da wata babbar sutura mai girma.


Burdah: Wannan tufa wani abu ne da mutum ke lullube kansa. Nana A’isha, Allah Ya yarda da ita, ta saka wa Annabi burda baka kuma ya sanya ta. Hakanan wata bai wa ta ba shi kyautar Burdah ya karba. Ya mallaki wasu korayen burda guda biyu da aka fi sani da Habrah. Har ila yau, a zamanin jahiliyya ana amfani da Burdah a matsayin mayafi da rana, da kuma abin rufa da dare. Daya daga cikin mashahuran burdajin Manzon Allah (SAWW) an baiwa Ka'b bin Zuhair kyauta, saboda wata waka da ya yi ta yabon Annabi. Daga baya Muawiyah ya saye wannan burda, ta zauna tare da khalifofin Abbasiyawa har zuwa lokacin da Mongolawa suka mamaye Bagadaza, sai Hulagu ya ba da umarnin a kona ta; duk da haka, ance ba a kona ta ba, amma sun tafi da ita a matsayin ganima.


Jubba: Wannan tufa ce mai kama da rigar zamani mai dogon hannu, yawanci ana buɗe ta, ta gaba kuma ana sawa a kan kaftan. An yi ta da don lokacin hunturu. A Makka, ana sanya ta a jiki, an yi ta daga yadudduka masu haske da alharini, kuma cikakkiyar sutura ce da ba ta buƙatar sanya wani abu tare da ita. An ruwaito cewa Annabi Muhammad ya yi salla tare da sahabbansa, sanye da jubbansa ita kadai. Ya ƙi jubba ɗin da aka yi da siliki. Wani nau'in jubba yana da maɓallin siliki. Wani mutum ya zo wurin Annabi yana sanye da jubba irin wannan, sai Annabi ya soke ta, yana nuna cewa irin wannan tufafin ba shi da kyau. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya na sanya jubba a lokacin tafiya.


Habrah: Wannan nau'i ne na tufafin Yaman, yawanci ana yafa ta ne, kuma ta na cikin irin tufafin da Annabi ya fi so. Ba takamaimen tufafi bane, amma kayan ado ne da a ke sakawa a kan tufafi. Annabi ya na lullube da ita da riga Habrah a lokacin wafatinsa, kuma an sanya mata su na Habrah don adonta, kuma tana daga cikin manyan tufafin Larabawa. Yawanci koriya ce kuma an yi da audugar da aka saƙa.


Hullah: Wannan ana hada ta ne da izar da alkyabba, ana kiransu tufa daya. Manzon Allah (SAWW) ya saka jar Hullah. Aisha ta yi masa guda daya, wanda ya daina sakawa bayan ya lura tana sa shi zufa saboda ulu.


Khamisa: Wannan baƙar tufa ce. A’isha ta ruwaito cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) zai yi salla a da wata Khamisa, sai ya nemi ya musanya ta da wata riga. Wasu sahabbai sun ganshi yana sallar rokon ruwan sama sanye da bakar khamisa, Anas ya ruwaito cewa a lokacin da mahaifiyarsa ta aike shi wurin Annabi, domin Annabi ya ganshi, Annabi yana sanye da khamisa daga Huraith.


Rida: Wannan tufa ce da ake sawa a kan wasu tufafi kamar alkyabba kuma tana rufe saman jiki. Aisha ta ruwaito, Annabi yana lullube ta da Rida. Ya na kuma sanya Najrani Rida, da Hadrami rida, da rida ta kurdish, musamman a lokacin da ake addu’o’in rokon ruwan sama da lokacin shiga haramin aikin hajji. Tsawon Rida ɗinsa kamu shida ne da yatsu uku, kuma Izar ɗinsa ta Omani kamu huɗu ce.


Sarawil: Wannan tufa ta na rufe kasan jiki kuma haramun ne ga masu Ihrami. An ruwaito cewa Annabi ya sayi sarawila ya rabawa sahabbansa, suna sawa da izininsa.


Shamla: Larabawa sun kasance suna lullube kansu da wannan rigar da daddare idan suna barci. Idan shamla ta yi girma ana ce da ita Nimra. Manzon Allah ya sa shamla kafin lokacin aiko shi, lokacin da ya halarci aikin sake gina Ka'aba. Ana daukar ta a matsayin tufafin da talaka ke sawa.


Qaba: Wannan kalma ce ta Farisa ta buɗaɗɗiyar riga da ake ɗaure wa da bel, da ake sawa a kan wasu tufafi. Ana kiranta da rigar fulawa. Annabi ya raba wasu Qaba a tsakanin sahabbansa amma da farko bai zabi tasa ko daya ba, daga baya ya bayyana cewa ya kebe wa kansa daya ta musamman.


Qamis: Wannan sutura ce da aka dinka da hannun riga, da ake sawa a karkashin wasu tufafi, kuma yawanci an yi ta da auduga, ko ulu. Yana daga cikin tufafin da Annabi ya fi so. An gan shi yana sallar jana'iza sanye da qamishi biyu, kuma a lokacin yakin Badar baffansa Abbas ya ba shi kyautar kamis daga Abdullahi bin Ubay.


Kisaa: Wannan kalma tana nufin duk wata sutura da aka yi ba don amfanin ɗan adam kaɗai ba. Tana iya rufe komai tun daga Ka'aba zuwa doki ko rakumi, da gadaje da kujeru. Anas bin Malik ya ga Annabi yana amfani da Kisa’a wajen salla da kuma kariya daga zafi da sanyin kasa. Daga cikin nau’o’in Kisa’a akwai abaya, da aka yi da ulu, a bude ta, ta gaba, ana sawa a kan wasu tufafi. An karbo hadisi daga Yazid bin Sharik ya ce, Annabi ya bar shi ya sanya abaya da ya kasance yana salla a cikinta, ya kwana a cikinta har sai gari ya waye.


Launukan Tufafin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama


Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya sanya riguna masu kore, baki, da masu ratsin baki da fari, da rawaya, da fari, wanda shi ne launin da ya fi so. Ya kwadaitar da sahabbansa madaukaka da cewa: "Ku sanya fararen tufafi, ku tufatar da rayukan ku a cikinsu, kuma ku lullube matanku da su, domin su ne mafi kyawun tufafinku".


Don haka sanya fararen tufa yana daga cikin Sunna, kuma sanya wasu launukan ya halatta. An sami sabani game da launin ja; wasu sun kyamace shi, wasu kuma sun halatta, a bisa wan hadisin: "Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fito sanye da jar Hula". Ya hana sanya tufafin da aka rina da safflower ko saffron. (Wasu nau'ikan fulayoyi ne da ban san su da hausa ba).


Muhimmancin Tufafi A Musulunci


A harshe, ana siffanta tufafi da duk wani abu da ya lulluɓe jikin ɗan adam, walau tufafi ko waninsa. Annabi (SAWW) yace, “Ni na sanya tufa, kuma ina tufatar da wasu”, abin da ake sawa kuma shi ake ce masa “libas” (tufafi). Muhimmancin tufafi yana bayyana yayin da ake nuna wayewa, birnanta, da mutunta kai. Haka nan yana daga cikin ni'imomin da Allah ya yi wa 'yan Adam, da kare su daga fitintinu da waswasin Shaidan wadanda ke kiransu zuwa ga cire tufafi.


Allah Ta’ala yana cewa: “Ya ku ‘ya’yan Adam, mun sanya muku tufa da za su tufatar da al’aurarku, kuma abin ado, amma tufar takawa, ita ce mafi alheri. Wata ayar kuma tana cewa: Ya ku ‘ya’yan Adam! Kada Shaidan ya jarabce ku, kamar yadda ya fitar da iyayenku daga Aljanna, yana mai tube musu tufarsu domin ya nuna musu al’aurarsu, (Quran 7:26-27). Don haka magana ta zama ta gama gari ga dukkan bil’adama, yadda Allah Ya yi musu ni’ima da abin da ya lullube jikinsu.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel