Ramadan: Abubuwa Goma ga Ma’aurata a lokacin azumi — kashi na 2 - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Ramadan: Abubuwa Goma ga Ma’aurata a lokacin azumi — kashi na 2

Ramadan: Abubuwa Goma ga Ma’aurata a lokacin azumi — kashi na 2

 Ramadan: Abubuwa Goma ga Ma’aurata a lokacin azumi — kashi na 2


Assalamu alaikum. Barka da sake saduwa a cikin wannan shafi. Da fatan Allah Ya sanya mu sami amfana da duk bayanan da za su zo ciki, amin.


Ga ci gaba da bayani kan abubuwa goma da ma’aurata za su iya yi a cikin Ramadan don ƙara samun shakuwa da farin ciki.


4. Salon Buɗa Baki 

Ma’aurata za su yi amfani da lokacin buɗa baki don ƙara kusanci, farfaɗo da sha’awa a cikin zuciyoyinsu. Su tsara buɗa bakinsu ta yadda za su zama kamar sabbin masoya ne cikin sabuwar soyayya.


Su buɗa baki cikin wasa da raha, ciyar da juna abinci, kallon marmasar soyayya, da kiran juna sunayen soyayya masu ƙayatarwa. Wannan zai ƙara ƙaunar juna da nishadi.


5. Wasanni 

Don ƙara kusanci da nishadi, ma’aurata za su yi amfani da wasanni na baka, na jiki, da na kwakwalwa. Misali, a yammacin rana lokacin da uwargida ke aikin gida, maigida zai iya ɗaukar lokaci don yin wasa kamar: "Na fi son ki saboda kaza da kaza." Ita ma za ta ba shi amsa da irin wannan wasan.


Bayan buɗa baki kafin lokacin Tarawihi, za su iya yin wasan tsere, tsalle, ko wasu wasannin da suka dace. A karshen mako kuma, za su iya shirya wasan tambayoyi kan ilimi, kamar game da Ramadan, Alƙur’ani, ko tarihin Annabi Muhammad (SAW). Wanda ya ci za a ba shi kyauta.


Waɗannan wasanni suna da muhimmanci wajen ƙarfafa dangantakar aure, kuma za su kara farin ciki mai dorewa a cikin zuciyoyinsu.


6. Ɗauke Nauyi 

Ma’aurata za su duba abubuwan da ke da nauyi ga juna su taimaka wajen sauƙaƙa waɗannan nauyi. Misali, maigida zai iya taimaka wa uwargida wajen shirya abincin buɗa baki, ko uwargida ta taimaka wa maigida wajen wasu ayyuka.


Idan maigida ya ga cewa uwargida ta gaji, zai iya ba ta damar hutu, ko kuma uwargida ta ba maigida kyauta don ƙarfafa shi wajen hidimar azumi da sallah.


7. Sadaukarwa 

Ma’aurata za su nuna sadaukarwa ta hanyar yin abubuwa masu mahimmanci ga juna. Misali, maigida zai iya taimaka wa uwargida wajen aikin gida, ko uwargida ta ba maigida damar yin ibada cikin kwanciyar hankali.


Sadaukarwa ta ƙunshi yin abubuwa marasa sauki don faranta wa abokin aure rai, da kuma yafe wa juna kurakuren da suka yi.


8. Tunatarwa 

Ma’aurata za su yi tunatarwa ga juna game da abubuwan da suka shafi addini, ɗabi’a, da zamantakewa. Misali, idan maigida ya ga cewa uwargida ba ta yin sallah cikin lokaci, zai iya yi mata nasiha mai kyau.


Za su yi amfani da hanyoyi masu kyau wajen ba da nasiha, kamar ta hanyar magana, rubutu, ko sakon waya. Ba za su yi zargi ba, sai dai nuna illolin rashin yin aikin da ya dace.


9. Romansiyya 

Ma’aurata za su ƙara ƙauna ta hanyar yin abubuwan romansiyya. Misali, maigida zai iya rufe idan uwargida yayin da take aiki a kicin, ko uwargida ta rubuta wasiƙar soyayya ta sanya a cikin aljihun maigida.


Wasanni kamar "Na fi son ki saboda kaza da kaza" su ma suna cikin ayyukan romansiyya da za su iya yi.


10. Yin Ibadar Tare 

Wannan shi ne mafi muhimmanci daga cikin abubuwan da suka gabata. Ma’aurata za su yi ibadarsu tare, kamar karatun Alƙur’ani, tasbihi, da sallah. Maimakon maigida ya yi tasbihi da yatsunsa, zai iya yi da yatsun uwargida, ita ma haka.


Za su iya yin musafar Alƙur’ani tare, inda ɗaya ya karanta, ɗaya ya saurara ko karanta fassarar ayoyin. Wannan zai ƙara haɗin kai da kusancin su da Allah.


Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kowane lokaci, amin. Sai mako na gaba in sha Allah.


Related Posts:
Previous article
This Is The Newest Post
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel