Ramadan: Abubuwa Goma Don Ma’aurata a watan Azumi
![]() |
Ramadan: Abubuwa Goma Don Ma’aurata a watan Azumi |
Ramadan wata ne mai tsarki da aka keɓe don ibada da neman kusancin Allah da tsarkake ruhi.
Assalamu alaikum. Barka da sake saduwa a cikin wannan shafin. Da fatan Allah Ya sanya mu cikin masu amfana da duk wani bayani da zai fito a cikinsa, amin.
Ina mika muku barka da zuwan watan Ramadan, watan alfarma da rahama. Da fatan Allah Ya sa mu dace da dukkan alherinsa kuma Ya sa mu zama daga cikin bayinsa da aka ’yantar, amin.
Abubuwa Goma ga Ma’aurata a watan Ramadan
1. Gyaran Aure
Ramadan lokaci ne na ibada da kyautata ayyuka. Aure da zamantakewar aure ɗaya ne daga cikin manyan ibadoji a addinin Musulunci. A cikin wani ingantaccen Hadisi, Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce, "Aure rabin addini ne." Don haka, kamar yadda muke ƙoƙarin inganta alakar mu da Allah, ya kamata ma’aurata suyi amfani da wannan watan don gyara alakar su da inganta zamantakewar su.
Bayan tsayawa kan ayyukan ibada kamar salla, karatun Alkur’ani, da Tarawih, ya kamata ma’aurata su duba wasu ayyuka na zamantakewar aure da suka manta ko kuma suka yi watsi da su, su gyara su.
Haka kuma, kamar yadda muke yawan yin istighfari da tuba a cikin Ramadan, ya kamata ma’aurata su koma ga abokan aurensu, su nemi gafara a kan abubuwan da suka aikata na rashin adalci ko kuskure. Sannan su juya su nemi gafara daga abokan aurensu a kan abubuwan da suka yi musu. Wannan zai kawo sauki da farin ciki a cikin rayuwar aurensu, kuma zai sa ibada ta zama mai daɗi.
2. Ibadar Aure
Ramadan wata ne da aka keɓe don ibada da neman kusancin Allah. Muhimmin abu shi ne a haɗa wannan wata tare da inganta ibadar aure. A cikin Alkur’ani, bayan Allah Ya yi magana game da Ramadan, sai Ya yi magana game da addu’a.
Aya ta 187 daga Suratul Baqarah ta ce: "An halatta muku a daren azumi yin jima’i zuwa ga matanku. Su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su. Allah Ya sani cewa kun kasance kuna yaudarar kanku, saboda haka Ya karɓi tubarku kuma Ya gafarta muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nemi abin da Allah Ya rubuta muku. Ku ci ku sha har sililin fari ya bayyana daga sililin baki a alfijiri, sa’an nan ku cika azumi har dare. Kada ku rungume su alhalin kuna cikin itikafi a masallatai. Waɗannan iyakoki ne na Allah, don haka kada ku kusance su. Kamar haka ne Allah Yake bayyana ayoyinSa ga mutane, tsammaninsu za su yi taƙawa."
Wannan aya ta nuna muhimmancin ibadar aure tsakanin ma’aurata. Don haka, ya kamata ma’aurata su inganta wannan ibada tare da sauran ayyukansu a cikin wannan wata mai alfarma.
Azumi yana tsarkake jini, yana share dattin abubuwa a cikin kwakwalwa, kuma yana gyara manyan sassan jiki, gami da na’urorin sha’awa. Haka kuma, canjin abinci ta hanyar yawan cin ’ya’yan itace da kayan lambu yana taimakawa wajen inganta sha’awa. Don haka, ya kamata ma’aurata suyi amfani da wannan dama don inganta ibadar aurensu a cikin Ramadan.
3. Kyaututtuka da Soyayya
Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce: "Ku yi musayar kyaututtuka tsakaninku, sai ku ƙara ƙaunar juna." Wannan kyakkyawar Sunnah ce da ya kamata ma’aurata suyi a cikin wannan watan Ramadan don ƙara ƙauna da soyayya a cikin aurensu.
Ba lallai ba ne kyautar ta kasance mai tsada, ko da ƙaramin abu ne, muddin yana nuna soyayya da kulawa. Misali, maigida zai iya kawo uwargidansa wata cakwalet mai daɗi, ko kuma uwargida ta shirya wani abinci na musamman da mijinta yake so.
Da fatan Allah Ya sa mu ci gaba da kasancewa cikin kariyarSa a kowane lokaci.
Amin.
Leave Comments
Post a Comment