Hukuncin Azumin Yaran da suka Balaga da Wuri - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Hukuncin Azumin Yaran da suka Balaga da Wuri

Hukuncin Azumin Yaran da suka Balaga da Wuri

 Hukuncin Azumin Yaran da suka Balaga da Wuri


Ko da yake azumin Ramadana bai zama wajibi ba ga yaran da ba su balaga ba, ana ƙarfafa iyaye da su fara koya musu yin azumi tun kafin su kai matakin balaga.


Azumi É—aya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, wanda ke nufin ya zama wajibi a kan kowane Musulmi baligi mai lafiya.


Azumin bana ya fara ne daga ƙarshen watan Fabrairu zuwa ƙarshen watan Maris, kuma ana sa ran za a yi shi cikin yanayin zafi.


Azumi yana É—aya daga cikin abubuwan da yara ke son yin su tare da Sallar Idi. Sai dai wasu iyaye kan hana su cika azumin kamar na manya, ko da sun kai matakin balaga.


Menene addinin Musulunci ya ce game da azumin irin wannan rukuni na yara? Kuma ta yaya ya kamata su fara yin azumi?


Matakan Balaga a Shari'ar Musulunci 

Yawanci wannan yanayi ya fi shafar yara mata, waɗanda sukan fara jinin al'ada a ƙananan shekaru.


Idris Mainasara Gandun Albasa, malamin addinin Musulunci a jihar Kano, arewacin Najeriya, ya bayyana cewa akwai matakai da ake bi don gane ko yaro ya balaga ko a'a.


"A mazhabar Malikiyya, yarinya mace tana balaga ne daga lokacin da ta kai shekara 9. Wannan yana nufin cewa sallah da azumi sun zama wajibi a kanta. Amma idan ta fara jinin al'ada kafin shekara 9, to sallah da azumi sun zama wajibi a kanta," in ji shi.


"Na biyu, za a iya gane mace ta balaga idan ta É—auki ciki ko da ba ta fara jinin al'ada ba. Idan haka ta faru, ana yi mata hukunci da ta kai matakin balaga ko da ba ta fara jinin ba."


Na uku kuma, akwai abin da ake kira "attamyeez," a cewar malamin, wanda ke nufin kaiwa shekarun hankali a bayyane.


"Ana nufin idan alamun girma suka bayyana a jikinta, kuma aka lura tana da hankali, to ana É—aukar ta balaga. Haka ma namiji yana bin wannan hukuncin idan alamun girma sun fito masa, kamar gemu ko gashin baki."


Menene Hukunci? 

Don samun ƙarin bayani game da hukuncin da shari'ar Musulunci ta tanada a kan wannan batu, mun tuntubi Malam Abubakar Abdullahi Goron Namaye daga jihar Kaduna.


Malam ya ce addinin Musulunci bai damu da girman jikin yara ba wajen tantance balagarsu.


"Matuƙar mace ta fara jinin al'ada, to duk abin da ya wajabta ya hau kanta," kamar yadda malamin ya bayyana.


"Idan ka duba labarin auren Nana Aisha da Annabi Muhammad (SAW), ba ta wuce shekara 9 ba. Sannan akwai wani hadisi da ke cewa, 'Ku umarci 'ya'yanku da su yi sallah tun suna shekara 7, kuma ku doke su idan sun kai shekara 10 basa yin sallah.'"


"A taƙaice, idan balagar ta bayyana, to azumi ya zama wajibi a kan yaron, matuƙar dai yana da lafiyarsa, ko da kuwa girman jikinsa bai kai ba."


Sai dai Malam Idris Mainasara ya ce yana ba iyaye shawarar su yi ƙoƙarin koya wa yaran azumi tun kafin balagar ta same su.


"Abin da malamai ya kamata su fadakar da iyaye shi ne, iyaye su dinga ƙarfafa yara wajen yin azumi, ba wai lokaci ɗaya ba a ce su fara yin azumi," in ji shi.


"Sannan wani lokacin yana da kyau a nemi shawarar likitoci don duba yanayin yaro. Sannan kuma a nemi fatawar malamai kan kowace matsala don samun mafita."


Dabarun Koya wa Yaro Azumi 

Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen koya wa yara yin azumi, ko da kuwa bai kai cikakken azumi ba.


Ɗaya daga cikinsu ita ce ɗaukar azumi daga farkon rana zuwa tsakiyar wuni, ko da yake wasu yaran kan nemi a ƙyale su su kai har ƙarshen rana. Amma ana shawartar iyaye da su bi wannan a hankali don kada yaro ya gaji sosai.


Haka kuma, idan yaro ya nuna cewa zai iya ɗaukar azumi daga farkon rana zuwa ƙarshen wuni, za a iya saka shi ya yi azumi kwana ɗaya ko biyu a mako.


A gefe guda kuma, wasu iyaye kan bari yaran su yi azumi na wani ɗan lokaci amma su huta a cikin kwanaki 10 na ƙarshe.


"Tun da azumin bai wajabta a kansu ba, ana bai wa iyaye damar yin ibadar yaran," in ji Malam Abubakar Goron Namaye.



Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel