Bayani kan Hukunce-hukuncen da suka shafi azumin matafiya
![]() |
Bayani kan Hukunce-hukuncen da suka shafi azumin matafiya |
Ko da yake azumin watan Ramadana ya zama wajibi ga dukkanin mabiya addinin Musulunci, akwai rangwamen da aka yi wa matafiya, inda suke da damar ajiye azuminsu a lokacin da suke balaguro.
Azumin Ramadana yana daya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, wanda ya hada da gaskatawa da Allah, amincewa da Annabi Muhammadu (SAW) a matsayin manzon Allah, imani da kaddara, da kuma aikata Hajji ga wanda ya sami damar yin sa.
Musulmai kan yi azumi tsawon kwana 29 ko 30 a cikin watan Ramadana, wata na tara a kalandar Hijira, inda suke hana kansu cin abinci da sha daga fitowar rana zuwa faduwarta.
Akwai wasu rukunnan mutane da yanayi da aka bai wa rangwame a cikin azumin, ciki har da matafiya.
Wace irin tafiya ce za ta sa mutum ya ajiye azumi? Kuma yaushe ya kamata ya rama?
Mun tuntubi malamai domin samun amsa ga wadannan tambayoyi da sauransu.
Shin ajiye azumi wajibi ne ga matafiyi?
Rangwamen da aka bai wa matafiya na ajiye azumin Ramadana ya samo asali ne daga ayar Alkur'ani da ta ce marasa lafiya ko matafiya za su iya ajiye azumi, kamar yadda Dr. Yahaya Gwani Yahuza, malami a sashen darussan Musulunci na Jami'ar Bayero, ya bayyana wa BBC.
"An bai wa mutane wannan damar domin su rama azumin a wani lokaci nan gaba," in ji shi.
Duk da haka, malamai sun sha bamban kan ko dole ne matafiyi ya ajiye azumi yayin balaguro.
"Wasu malamai suna ganin cewa dole ne mutum ya ajiye azumi idan zai yi tafiya. Sun kafa hujjarsu da hadisin Annabi Muhammadu (SAW) da ya ce 'ba shi daga cikin da'a mutum ya yi azumi a lokacin tafiya,'" in ji Dr. Yahaya.
"Amma mafi yawan malamai suna ganin ajiye azumi sauqi ne daga Allah. Wanda ya ajiye ya kyauta, wanda kuma ya yi azuminsa bai yi laifi ba."
A gefe guda, Sheikh Idris Mainasara Gandun Albasa ya ce idan aka yi la'akari da ayar Alkur'ani, za a ga cewa "yin azumi ya fi alheri ga matafiyi".
"Sai dai kuma ajiye azumi sassauci ne da Allah ya bai wa mutum, kuma Allah na son idan ya bayar da sassauci a karɓa. Matukar mutum ya san zai sha wahala ko yaya ne a tafiyar, to yana da dama ya ajiye," in ji malamin daga jihar Kano.
Wace irin tafiya ce aka yarda mutum ya ajiye azumi?
Fatawowin da malaman addinin Musulunci suka bayar ta nuna cewa ba kowane balaguro ne ko tafiya suka cancanci mutum ya ajiye azumi ba.
Dr. Yahaya ya ce za a ajiye ne kawai a tafiyar da ta dace a yi wa kasaru - wato taƙaita salla mai raka'a huɗu zuwa raka'a biyu.
"Tafiyar da ta cancanci a yi wa kasaru kuma ita ce mai tsawon kilomita 83, ko kuma mil 43," in ji shi.
Sheikh Mainasara ya tabbatar da hakan, inda ya ce "duk wanda zai yi tafiyar da ta kai kilomita 80 zuwa sama zai iya ajiye azumi."
Yaushe ne matafiyi zai ajiye azumin?
Akwai yanayin da mutun zai shiga na kula game da yiwuwar tafiyar tasa. Sheikh Mainasara ya ce a irin wannan yanayin mutum ba zai ajiye azumi ba.
"Sai mutum ya fara tafiya zai ajiye azumi. Da ma ko sallar kasaru, an ce sai mutum ya wuce gonakin garinsu sannan zai fara yin ta.
"Saboda haka, ba wai tun daga lokacin sahur mutum zai É—auki niyyar ajiye azumi ba. Za a É—auki azumi har sai tafiya ta tabbata tukunna, har ma sai mutum ya je tashar jirgi ko mota, an fara tafiya sannan zai ajiye azuminsa."
Da wane lokaci matafiyi zai yi aiki wajen bude-baki?
Akan samu lokutan da matafiyi zai bar ƙasarsu bayan an ga watan sallah - ma'ana an gama azumi baki ɗaya - amma ya isa ƙasar da ya nufa kuma ya tarar ba a ga watan ba. Me mutum ya kamata ya yi a irin wannan yanayi?
Dr. Yahaya ya bayar da amsa da cewa: "ÆŠaya daga cikin sharuÉ—É—an azumin Ramadana shi ne niyya, shi kuma bai É—auki niyyar yin azumi ba.
"Saboda haka hukuncinsa shi ne, zai kame bakinsa ya ci gaba da azumi, kuma zai ajiye azumin ne tare da mutanen garin da ya je, ba in da ya baro ba.
"Idan kuma ya tarar sun ajiye azumi suna yin Idi a daidai lokacin da shi kuma azuminsa bai kai 29 ba, to zai ajiye azumin sannan kuma ya rama sauran bayan sallah."
Kazalika, wannan hukuncin ya shafi wanda ya bar ƙasarsu bayan an sha ruwa kuma ya isa ƙasar da rana ba ta fadi ba.
Shin hukuncin É—aya ne da matafiyi a jirgi?
Malamai sun ce babu bambancin hukunci game da abin da aka yi amfani da shi wajen yin balaguro.
"A tsarin Musulunci, da wanda yake tafe a jirgi, da na mota, da na dabba, idan ya cika sharuÉ—in kasancewarsa matafiyi to hukuncin iri É—aya," in ji Sheikh Mainasara.
Shi ma Dr. Yahaya ya tabbatar da hakan. "Abu mafi muhimmanci dai shi ne ya zamana ya cika sharuÉ—in yin tafiyar," in ji shi.
Leave Comments
Post a Comment