Abubuwa biyar da ba su karya azumi, Fatawar Sheikh Jabir Maihula
![]() |
Sheikh Dr. Jabir Maihula |
Akwai sharuɗɗa da ƙa'idodi da suka shafi kowace ibada a addinin Musulunci, ciki har da azumin Ramadan wanda yana ɗaya daga cikin rukunan addinin. Babban abin da mai azumi zai guje wa yayin azumi shi ne cin abinci da sha tun daga fitowar rana har zuwa faɗuwarta, duk da cewa akwai wasu sharuɗɗa da ladubba.
Sai dai akwai wasu abubuwa da wasu mutane ke tunanin suna karya azumi, amma ba haka ba ne. Sheikh Dr. Jabir Maihula, wanda malamin addinin Musulunci ne a jihar Sokoto, arewacin Najeriya, ya lissafta wasu abubuwa biyar da jama'a da yawa ke zaton suna karya azumi, amma ya ce ba su karya azumin ba.
1) Fitar Maziyyi
Daga cikin abubuwan da mutane ke tunanin suna karya azumi akwai fitar maziyyi. A cewar malamin: "Maziyyi shi ne abin da ke fita daga gaban namiji ko mace saboda sha'awa, ba lokacin jima'i ba. Wani lokaci yakan fita daga jikin mutum ba tare da saninsa ba, saboda yakan fita ne kaÉ—an-kaÉ—an. Yawancin lokuta sha'awa ta kallon wani abu da ido ke haifar da shi. Bisa fatawa mafi inganci, fitar maziyyi ba ya karya azumi."
2) Amfani da man goge baki
Da yawa masu azumi kan guje wa yin amfani da man goge baki saboda tsoron karya azumin. Wani lokacin kuma wasu masu azumi ba sa son amfani da shi saboda ka da "warin bakin mai azumi" ya tafi ba tare da samun lada ba. Amma Sheikh Maihula ya ce: "Duk malaman wannan zamani, kamar bin Uthaimin, bin Baz, da kwamitocin fatawa na duniya, sun ce amfani da man goge baki ba ya karya azumi. Saboda ba abin ci ba ne, ba abin sha ba ne, kuma ba shi kaiwa ciki – sai dai idan mutum ya haÉ—iye shi da gangan."
3) ÆŠaukar jini ko allura
Sheikh Jabir ya ce, ban da amfani da man goge baki, akwai wasu abubuwa da suka shafi lafiyar ɗan adam waɗanda ba su karya azumi idan aka yi su. "Misali, ɗaukar jini daga mutum idan ba shi da lafiya domin a yi gwaji. Wannan ba ya karya azumi." Malamin ya kara da cewa: "Muna ba da shawarar kada mutum ya ba da jini domin a ƙara wa wani, saboda akwai saɓani mai ƙarfi a tsakanin malamai game da hakan, saboda yawan jinin da mutum zai ba." Haka nan, yi wa mutum allura ba ya karya azumi, amma da sharaɗi. "Amma kada allurar ta zama madadin abinci. Misali, akwai mutanen da ba su iya cin abinci ko sha, sai a yi musu allura a madadin haka."
4) Maganin shaƙa na asma
Sheikh Maihula ya kuma bayyana cewa amfani da maganin shaƙa da masu cutar asma ke amfani da shi (inhaler) ba ya karya azumi. "Saboda ba abinci ba ne, ba abin sha ba ne, kuma ba shi kaiwa cikin mutum. Ko da mutum ya ji shi a maƙogwaronsa, ba zai karya masa azumi ba."
5) Maganin ciwon ido
Haka kuma, amfani da maganin da ake ɗigawa a ido saboda wani ciwo ba ya karya azumi, in ji Sheikh Maihula. "Ko da mutum ya ji shi a maƙogwaronsa, ba zai karya azumi ba, saboda ba abinci ba ne, ba abin sha ba ne, kuma ba shi kaiwa ciki."
Ta haka ne, Sheikh Dr. Jabir Maihula ya fayyace wasu abubuwa da yawa ke zaton suna karya azumi, amma a haƙiƙa ba su karya azumi ba. Yana da muhimmanci ga masu azumi su fahimci waɗannan abubuwa domin su guje wa ɓata azuminsu ba da gangan ba.
Leave Comments
Post a Comment