Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa

Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa

Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa  


Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana wasu muhimman abubuwa da ya kamata mai azumi ya yi a watan Ramadan. 


Yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar azumi, Sheikh Daurawa ya nuna cewa akwai lada mai yawa ga wanda ya aiwatar da waɗannan ayyuka:  


1. Azumi: Mai azumi ya kamata ya kula da azuminsa, ya fahimci hukunce-hukuncensa, ya kiyaye su, tare da guje wa abubuwan da zasu rage lada ko karya azumi.  


2. Sallah: Ya kamata a dage da yin Sallolin Taraweeh da Tahajjud, tare da kiyaye sallolin farilla a cikin jam’i da kuma yin nafiloli da ake yi kafin ko bayan su.  


3. Ciyarwa: Ciyarwa tana da matuƙar muhimmanci, ko da dabino ko ruwan sanyi ne. Sheikh Daurawa ya ambaci hadisin Annabi (SAW) cewa: “Duk wanda ya ciyar da mai azumi, za a ba shi lada kamar ya yi wani azumin ne.”  


4. Umrah: Idan mutum yana da damar yin Umrah a watan Ramadan, yana da lada mai girma. Idan ba shi da damar, sai ya maye gurbinsa da ciyarwa.  


5. I’tikaf: Sheikh Daurawa ya ba da shawarar cewa Musulmi su shiga I’tikaf idan suna da damar hakan, domin su tsarkaka kansu da ibada tare da nisanci daga shagalin duniya.  


6. Daren Lailatul Qadar: Ya kamata Musulmi su dage da neman dacewa da daren Lailatul Qadar ta hanyar yin salloli, addu’o’i, da sauran ayyukan alheri.  


7. Yafiya: Sheikh Daurawa ya buƙaci Musulmi da su yafe wa juna, domin su sami gafarar Allah a cikin wannan wata mai alfarma.  


8. Karatun Alƙur’ani: Ya kamata Musulmi su ƙara karatun Alƙur’ani, domin Ramadan shine watan da aka saukar da shi.  


9. Addu’a: Yana da muhimmanci a dage da yin addu’a, musamman a lokacin Sahur, lokacin buɗa-baki, da lokacin da ake cikin azumi, domin a waɗannan lokuta Allah Yana karɓar addu’o’i.  


10. Zumunci: Sada zumunci a watan Ramadan yana ƙara albarka, arziƙi, da zaman lafiya, kamar yadda Sheikh Daurawa ya bayyana.  


11. Tausayi: Azumi yana koyar da tausayi da taimako, domin mai azumi zai ji halin da masu buƙata ke ciki, hakan zai sa ya fi jin ƙansu.  


Ta haka ne, Sheikh Daurawa ya ƙarfafa wa Musulmi su yi amfani da wannan wata mai tsarki ta hanyar yin waɗannan ayyuka masu muhimmanci, domin su sami lada mai yawa daga Allah (SWT).


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel