Sabon Haɗin Maganin gyaran nono — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Sabon Haɗin Maganin gyaran nono — Android Pols

Sabon Haɗin Maganin gyaran nono

Sabon Haɗin Maganin gyaran nono 



Maganin gyaran Nono na mata,wanda yake kara girma,da kuma yadda za'a rage idan bukatar hakan ya taso, domin ana samun matan dake bukatar su rage girman nono idan yai musu yawa. 


Domin gyara nono ga mata, Idan baku mantaba munyi muku alkawarin zamu kawo muku bayani akan yadda zaku magance zubewar nono masamman awajen mata wanda suke kasa da shekaru 39. 


Saboda mahimmancin gyaran jiki awajen mata musamman ma gyaran nono mun kawo muku bayanai akan yanayin gyaran nono, aciki mun ambaci cewa gyaran nono yakasu kashi uku:


- Nafarko shine karin girman nono.

- Nabiyu shine rage girman nono

- Na'uku shine mikar da nono.


Mun yi bayani akan na farko yau kuma za mu yi bayani akan na ukun wanda shine yadda za'a magance matsalar zubewar nono a wajen mata masu karancin shekaru, har yanzu sai abimu bashin nabiyun zuwa wani lokaci akusa.


Hakikanin gaskiya kowace mace tanaso taga tanada tsayayyen nono tsawon rayuwanta amma kash. Sai de hakan ba maiyuwa bane, sabida zubewar nono a dabi'ance yana faruwa tare da tafiyan shekaru.


Maganin sanyin kowanne iri


 kamar yadda aka sani duk lokacinda mace takai shekaru arba'in to gaskiya babu abinda zai hana nononta zubewa, saide matsalan ana iya samun dayawa mata wanda basukai wannan shekarunba kuma nononsu yazube, sannan yana daga cikin abubuwanda yake janyo zubewar nono kamar:


- shayarwa.

- Daukan ciki.

- Yankewar jinin haila gabadaya.

- Ramewa cikin dan kankanin lokaci.

- Kiba.

- Wasu cututtuka kamar cancer da sauransu.


A takaice zamu fadi hanyoyi guda uku na mikar da nono ba tareda shan wahala ko kashe kudi ba, nafarko:


1- A samu kankara a shafa a jikin nonuwan duka biyu, ake shafawa a hankali har ta shafa a ko'ina har na tsawon kamar minti biyu, za'a maimaita hakan na tsawon wasu kwanaki, kankara yanada tasiri sosai wajen matse nono da hanashi zubewa, amma kada yawuce minti uku tana shafawa daga bisani sai ta samu bra dedenta tasaka.


2- Nabiyu kuwa shine man zaitun, dayawa yan'uwa mata suna tareda man zaitun amma suna neman maganin zubewar nono, to wallahi kinbar magani mai mahimmanci sosai, anaso ki milke nononki daman zaitun kullum safe dayamma kishafa da hankali sannan atake kisaka bra wanda yadace dake. Za'a maimaita haka nawasu kwanaki, kuma za'a iya amfani da zaitu Lawz ko jojoba oil amadadin man zaitun.


3- Na'uku za'a iya hada neem oil tareda garin ruman cokali daya agarwaya wannan hadin sai adaura akan garwashi yadanyi zafi kadan sai asauke abarshi yahuce, daga bisani sai ake shafawa nonon sau biyu ayini zuwa wasu kwanaki kadan kuma wannan hadin yanada tasiri sosai.


 Za'a iya amfanida kowanne daga cikin wannan hanya guda uku domin gyaran nono kuma kowanne yanada tasiri insha Allah.



Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel