Maryam Malika Ta Nemi Kotu Ta Tabbatar Da Sakin Da Mijinta Ya Yi Mata
![]() |
Maryam Malika |
Jarumar fina-finai ta Kannywood, Maryam Muhammad, wacce aka fi sani da Maryam Malika, ta gabatar da bukata a gaban kotun shari’a da ke Magajin Gari, Kaduna, domin tabbatar da sakin da tsohon mijinta, Umar, ya yi mata.
A cikin shari’ar da aka yi a ranar Laraba, jarumar ta bayyana cewa mijinta ya furta saki na uku tun shekaru biyar da suka gabata, bayan ta nemi saki ta hanyar Khul’i (watau hakkin mace na neman saki a Musulunci). Lauyan jarumar, A.S Ibrahim, ya shaida wa kotu cewa mijin ya furta saki biyu ne kafin jarumar ta shigar da kara a kotu domin neman saki ta hanyar Khul’i.
“Bayan na shigar da kara, kotu ta aika wa mijina takardar umarni, kuma ya rubuta saki na uku. Duk da haka, ba a tabbatar da sakin a kotu ba, kuma jarumar ta ci gaba da harkokinta ba tare da tabbataccen saki ba,” in ji lauyan.
A yayin shari’ar, wanda ake kara ba ya cikin kotu, kuma bai aika wakili ba. Alkalin kotu, Kabir Muhammad, ya tambayi manzon kotu ko ya kai wa wanda ake kara takardar umarni, amma manzon ya bayyana cewa wanda ake kara ba ya gida a lokacin da ya je kai masa takardun.
Saboda haka, alkalin kotun ya umurci jami’an kotun da su sake aika wa wanda ake kara takardar umarni ta wasu hanyoyin da suka dace. Ya kuma dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.
Shari’ar ta nuna cewa jarumar tana neman tabbatar da sakin da aka yi mata, domin ta sami cikakken ‘yancin ta a bisa doka da kuma addinin Musulunci.
Leave Comments
Post a Comment