ABUBUWAN DA YAKAMATA KI SANI DA ZARAR KIN Haihu - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

ABUBUWAN DA YAKAMATA KI SANI DA ZARAR KIN Haihu

ABUBUWAN DA YAKAMATA KI SANI DA ZARAR KIN HAIHU
ABUBUWAN DA YAKAMATA KI SANI DA ZARAR KIN HAIHU


Akwai muhimmin abubuwan da kowace mace ya dace ta sani musamman wanda basu taba haihuwa ba. Ga jerin Abubuwan kamar haka; 


1. Ki fara shayar da jaririn ki da zarar kin haifeshi,kifara shayarda shi cikin awa dayan farko na rayuwarsa.


2. Ruwan nono shine abinci mafi kyau ga jariri wanda yake zuwa tatacce tare da dauke da duk wani abu da jariri ke bukata.


3. Ki shayar da jaririn ki safe da dare duk lokacin da ya bukata,Hakan zai taimaka miki wajen karuwar ruwan nono sannan ya kareki daga ciwo da kumburin nono


4. Shayar da jaririn ki cikin yan mintina kadan bayan haihuwa zai taimaka miki mabiyarki(placenta) ta fito da wuri sannan yarage miki zubar jini bayan haihuwa


5. Madarar dake fara fitowa bayan kinhaihu ba dattin nono bane,ki tabbata jaririnki yasha,wannan madarar itace rigakafi mafi muhimmanci da yaranki zai samu wanda zata fara bashi kariya daga ciwuka



Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel