Yaya Mace Za Ta Gane Ranar Da Take Yin Ƙwai da hanyoyin samun juna biyu?

Yaya Mace Za Ta Gane Ranar Da Take Yin Ƙwai da hanyoyin samun juna biyu?
Yaya Mace Za Ta Gane Ranar Da Take Yin Ƙwai da hanyoyin samun juna biyu? 


Yau a wannan darasin za ku ji bayani kan yadda mace zata gane ranar da take yin ƙwai da kuma hanyoyin da ma'aurata zasu bi domin samun juna biyu a cikin sauƙi (Ovulation and tips for getting pregnancy)


A yayin da samun juna biyu yakan zama kamar shan ruwa a wajen wasu ma'aurata, wasu ma'aurata suna shan wahala sosai kafin su samu dacewa. Samun juna biyu abu ne da ya ta'allaka da abubuwa da dama kamar irin su lafiyar mace, adadin shekarun ta, sanin kanta da wayewar ta, lafiyar namiji, yawan jima'i da dai sauransu. A cikin wannan rubutu za mu yi bayani kan yadda mace zata gane ranar da take yin ƙwai (ovulation) da kuma hanyoyin da mace zata bi domin samun juna biyu a cikin sauƙi.


Menene ake nufi da ovulation?

Ovulation shi ne fitar da ƙwai (egg) da yake faruwa a kowane wata daga ovary din mace. Wannan ƙwai shi ne tantanin halittar da mace ke bada gudunmawa domin samun juna biyu. Ana samun juna biyu ne idan wannan ƙwai ya haɗu da ɗaya daga cikin tantanin halittun dake cikin ruwan maniyyin namiji. Wannan haɗuwar itace ake kira da turanci 'fertilisation' wanda hakan shi zai sa ƙwan mace ya ƙyanƙyashe ta samu juna biyu.


Yaya mace ke yin ovulation?

Ko wace mace tana da ovary guda biyu a cikin kwankwasonta, waɗannan ovaries su ke da alhakin samar da ƙwai, fitar da shi da kuma samar da wasu sinadaran hormones na mata. Duk da cewa mace tana da ovary biyu amma a duk wata tana samar da ƙwai ƙwara ɗaya kacal. Ovaries ɗin guda biyu suna raba aiki a tsakaninsu, idan ovary ta farko ta samar da ƙwai a wannan wata toh wani wata mai zuwa ɗayan ce zata samar da ƙwai ita kuma ta farkon ta huta. 


Haka shine ɗabi'ar samar da ƙwai daga ovaries. Amma duk da haka wata rana wasu mata su kan sami ovaries dinsu duka biyu su samar da ƙwai a lokaci ɗaya, watau mace zata fitar da ƙwai biyu (2) kenan. Wannan shi ne asalin samun tagwaye (Dizygotic twins) idan har mace ta fitar da ƙwai biyu kuma ta samu yin jima'i a lokacin da duka ƙwan biyu ke raye kuma ko wane ƙwai ya samu haɗuwa da tantanin halittun dake cikin ruwan maniyyin namiji.


Mace tana samar da wannan ƙwai ne (tana yin ovulation) a tsakiyar watan ta na al'ada wanda yana kamawa ne bayan kwanaki goma (10) zuwa kwanaki goma sha biyu (12) bayan tayi tsarki daga jinin haila. Ko kuma ranar da zai rage saura kwanaki goma sha huɗu (14) chif kamin zuwan jinin hailarta na gaba.


Idan mace ta yi ovulation, ƙwan da ta fitar ya kan ɗauki tsawon kwanaki biyu (2) zuwa kwanaki uku kafin ya mutu, a lokacin da ƙwan ke raye shi ne kaɗai lokacin da mace zata iya samun juna biyu. Wannan shi yasa mafi kyawun lokacin da ya kamata mace tayi jima'i idan tana so ta samu juna biyu shi ne ranar da take tsammanin fitar da ƙwai (yin ovulation).


Amma duk da haka idan ta samu yin jima'i ko sau ɗaya ne a cikin kwanaki biyar (5) kafin tayi ovulation zata iya ɗaukar ciki saboda wasu tantanin halittun da ke cikin ruwan maniyyin namiji sukan ɗauki tsawon kwanaki biyar (5) zuwa bakwai (7) a cikin mahaifar mace suna neman ƙwai kafin daga baya su mutu. Haka kuma idan mace ba ta samu yin jima'i ba sai bayan kwanaki uku (3) da yin ovulation, toh ko sau nawa tayi jima'i a cikin kwanakin da ya rage ba zata samu ciki a wannan watan ba sai dai wani wata idan ta ƙare yin jinin al'ada. Abinda yasa haka shi ne, ƙwan da mace ke fitarwa baya iya wuce kwanaki uku bai mutu ba.


Akwai wani chamfi da mafi yawancin mutane suka ɗauka gaskiya ne, chamfin shi ne wai mace tana samun ciki ne idan tayi jima'i a ranar da ta ƙare yin jinin al'ada. Wannan magana ba gaskiya bace kuma babbar katoɓara ce a tsarin ilimin likitanci. Hasali ma, ranar da mace ta gama jinin al'ada ba zata iya samun ciki a wannan ranar ba, saboda akwai aƙalla kwanaki goma (10) kafin ta yi ovulation kuma tantanin halittun dake cikin ruwan maniyyin da zasu shiga mahaifarta idan tayi jima'in ba zasu iya kai kwanaki goma (10) basu mutu ba.


Menene Alamomin ovulation?

Kafin mace ta iya gane ranar da zata yi ovulation toh dole sai ta fahimci yanayin zuwan jinin al'adarta da kyau. Wannan shi yasa likitocin mata suke bada shawarar kowace mace ta rinka aje rekodin na yadda take yin jinin al'ada.


Kamar yadda muka yi bayani a baya, kwanakin da ake tsammanin mace zata yi ovulation su ne rana ta goma (10th) ko ta goma sha ɗaya (11th) ko ta goma sha biyu (12th) bayan ta gama yin jinin al'ada. A waɗannan kwanakin ana so ma'aurata masu neman haihuwa su dage da nema sosai.


Bugu da ƙari, akwai wasu alamomi da mace ke nunawa idan zata yi ovulation. Waɗannan alamomin sun haɗa da:


  • Zata ga wani ruwa mai yauƙi, marar kala yana yawan zuba daga farjinta.
  • Za ta iya jin wani ciwo kaɗan a gefen marar ta na hagu ko na dama.
  • Zata kama jin matsananciyar sha'awar jima'i.
  • Kan nonuwanta zai ɗan yi duhu kuma ya miƙe haka kuma idan aka taɓa akwai ciwo kaɗan.
  • Jikinta zai ɗan ƙara zafi.


Akwai wani gwajin fitsari da ake yi da wata takarda irin ta gwajin ciki wanda yake nuna mace ta kusan ovulation ko akasin haka. Ana kiran gwajin da turanci ovulation predictor test.


Hanyoyin samun juna biyu a cikin sauƙi 

Dagewa da yin jima'i a kwanakin da mace ke tsammanin ovulation.


Yin jima'i akai-akai da kuma ƙauracewa duk wata hanyar bada tazarar iyali; Masana sun fassara yin lafiyayyen jima'i akai-akai da yin jima'i sau biyu (2) zuwa uku (3) a cikin sati ɗaya. Sannan kwanakin jima'in kar su kasance suna bibiyan juna, anaso a bada tazara a tsakanin kwanakin domin namiji ya huta kuma ruwan maniyyinsa ya taru. Wannan shi yasa ba'a son namiji yayi jima'i kulli yaumin a jere sai a cikin kwanaki biyu ko uku da matarsa ke tsammanin ovulation. 


Anaso mace ta kwanta a bayanta na kamar mintuna goma (10) zuwa goma sha biyar (15) kafin ta tashi zaune bayan kammala jima'i. Yin haka shi zai ƙara bada dama ga tantanin halittun ruwan maniyyin namiji su shiga mahaifar mace.


Ƙauracewa matsanancin motsa jini: Matsanancin motsa jini yana da illa ga jikin mace, domin yakan iya hana ta samun juna biyu cikin lumana. Wannan shi yasa wasu mata masu ƙwallom ƙafa, ko masu gasar tseren mita ko mata sojoji suke samun matsalar haihuwa da yawan rikicewar jinin al'ada.


Ƙauracewa shan sigari da barasa.


Chin lafiyayyen abinci.


Ƙauracewa duk nau'in abincin ko abin sha da ke ɗauke da sinadarin caffeine.


Mace ta kula da jikinta kar tayi ƙiba sosai kuma kar ta zama siririya sosai.


A cikin wannan rubutu mun ga cewa mace tana samun juna biyu ne a lokacin da ƙwai da take fitarwa a lokacin ovulation ya haɗu da tantanin halittun dake cikin maniyyin mijinta. Haka kuma munga cewa fitar da wannan ƙwai yana faruwa ne a tsakiyar watan al'adar mace. Bugu da ƙari munga wasu hanyoyi da ma'aurata ya kamata su bi domin samun juna biyu cikin sauƙi.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post