Yanzu-Yanzu: Tanko Ya Musanta Zargin Da Ake Yi Masa Na Yin Garkuwa Da Kuma Kashe Hanifah - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Yanzu-Yanzu: Tanko Ya Musanta Zargin Da Ake Yi Masa Na Yin Garkuwa Da Kuma Kashe Hanifah

Yanzu-Yanzu: Tanko Ya Musanta Zargin Da Ake Yi Masa Na Yin Garkuwa Da Kuma Kashe Hanifah
Yanzu-Yanzu: Tanko Ya Musanta Zargin Da Ake Yi Masa Na Yin Garkuwa Da Kuma Kashe Hanifah


A ci gaba da shari'ar da Kotu ke yi akan Abdulmalik Tanko da wasu sauran mutane 2 da ake zargin su da yin garkuwa tare da kashe matashiyar yarinya Hanifah ƴar shekara 5. A zaman kotun da ya gudana ranar Litinin waɗanda ake tuhuma da aikata laifin sun musanta dukkan zarge-zargen da ake yi musu.


Kotun ta yi zaman ne bayan da gwamnati ta ɗaukar wa da waɗanda ake zargi lauya wanda a zaman ne shari'ar ne ƙarƙashin jagorancin Alƙali Usman Na-Abba. Inda aka lissafo musu zarge-zargen da ake yi akan su amma dukkan su sun musanta inda suka ce ba su aikata dukkan tuhume-tuhumen da ake yi akan su ba.


Alƙalin ya fara ne da Abdulmalik Tanko wanda shine ake zargin cewa ya sace Hanifah kuma yai garkuwa da ita inda ya nemi kuɗin fansa Naira miliyan 6 wanda kuma daga baya ya baiwa matashiyar maganin ɓera taci ta mutu. Hakan yasa ya kira abokin sa suka binne gawar Hanifah a harabar makarantar su.


Amma duka wannan zarge-zargen da aka lissafa wa Tanko ya musanta inda yace shi bai aikata ko ɗaya daga cikin Waɗanan laifinka ba. Haka su ma ana su ɓangaren Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin su ma duk sun musanta tuhume-tuhumen. Wanda hakan yasa kotun ta dage zaman shari'ar har zuwa sati mai zuwa domin tattara shaidu. 


Tun lokacin da aka hukumar tsaro ta samu nasarar kame Abdulmalik Tanko a lokacin da yaje ɗaukar kuɗin fansa da ya nema inda bayan bincike da aka gudanar ya bayyana cewa shine ya sace Hanifah kuma ya kashe ta. Bayan ya kashe ta kuma suka yayyanka jikin ta suka saka a buhu suka binne.


Wanda a lokacin da akai hira da shi da manema labarai ya bayyana cewa ya daɗe yana tarkon kama Hainfia domin yai garkuwa da ita ya samu kuɗi. A lokacin da ake hira dashi ya bashi ake bin sa masu yawa na hayar kuɗin makarantar da kuma hayar gidan sa.


Sai gashi kuma yanzu a kotu ya bayyana cewa bashi da masaniyar abinda ya faru da Hanifah kuma bashi da hannu akan abinda ya faru. Sai dai wannan al'amari ya baiwa jama'a da dama mamaki. Wasu na ganin cewa bai kamata ma a kawo har zuwa wannan lokacin ba tare da an yanke musu hukuncin abinda suka aikata ba.


Sai dai masana Shari'a na cewa dole ne sai anbi matakin yadda ake gudanar da ita ba wai kai tsaye ake yanke hukunci ba dole sai anbi mataki har zuwa lokacin da Alƙali ya gama tattara bayanai sannan kuma a yanke hukunci. Sannan anyi kira ga al'umma da su kwantar da hanklin su. 



Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel