YANDA ZAKI GYARA NONO (BREAST/BOOBS) SU TSAYA SU CIKO SUƘARA GIRMA - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

YANDA ZAKI GYARA NONO (BREAST/BOOBS) SU TSAYA SU CIKO SUƘARA GIRMA

YANDA ZAKI GYARA NONO (BREAST/BOOBS) SU TSAYA SU CIKO SUƘARA GIRMA
Gyaran nono 


Idan kina buƙatan gyaran nono su ciko su tsaya su ƙara girma akwai hanyoyi guda biyu da za ki bi, ma'ana zakiyi amfani da duka hanyoyi guda biyun domin samun sakamako mai kyau.


 NA FARKO (Haɗin Gayaran Nono Shafawa)  

ki gwada ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyin kamar haka;


1- A daka ƴaƴan hulba su zama gari sai a ɗebi garin a tafasa abarshi yaɗan huce sai asamu tsumma (towel) ƙarami adinga tsomawa a ruwan ana gasa nono, bayan an gama sai a wanke da ruwan ɗumi sannan a shafesu da man hulba asa brazia mai kama jiki


2- A zuba garin ƴaƴan hulba akofi azuba tafashashshen ruwan zafi kadan akwaba yayi kauri abarshi awa1 idan za'a kwanta bacci ashafawa nono asa leda anade su asa brazia mai kama jiki da safe a wanke da ruwan dumi ashafa man hulba.


3- Adaka kumfan maliya a kwaba da ruwan vinegar (Ma'ul khal) a shafawa nono a nade da leda asa brazia mai kama jiki. Wannan hadin yana gyara nono sosai. 


 HANYA TA BIYU (Haɗin Gyaran Nono NA SHA) 


Shima kigwada ɗaya daga cikin wadannan hanyoyin domin suna taimakawa wajen gyaran nono. 


1- Ahaɗa garin hulba da garin alkama ayi kunu asa madara asha.


2- Asamu Aya da Riɗi da gyaɗa a soya su sama-sama sai adaka ko aniƙa atankaɗe adinga ɗiba anasa madara da ruwan zafi a gauraya a sha


3- Asamu furen Tumfafiya da Nonon kurciya da kumbura fage da gadalin nono abusar dasu adaka atankaɗe adinga zuba garin a nono asha ko asa madara asa ruwan zafi agauraya asha.


TAMBIHI: wata da zaran ta fara cikin sati ɗaya zata samu yanda takeso wata kuma fiyeda haka saboda kowa da irin yanda jikinsa yake sannan idan kin gwada wannan bayyiba saiki gwada wani.


Wadannn sune hanyoyin yadda ake gyaran nono, da fatan za'a yi kokari a jarraba, sannan idan an dace a yi kokari sanarwa da sauran mata. 



Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel