Yadda Zaku Kare Kanku Daga Warin Baki A Yayin Da Kuke Yin Azumi |
Da yawa mutane na fama da matsalar warin baki wanda hakan ke jawo damuwa ga wanda suke da irin wannan matsalar. Wasu suna cewa duk da irin amfani da suke yi da abubuwan goge hakora amma dai basa samun wani sauyi daga bakin na su.
Wasu kuwa kaji suna cewa a rana sai su wanke baki sama da 10 amma kuma dai babu wani sauki, ma'ana dai warin baya dainawa. Wasu kuwa za kaji sun ce har irin wannan alawar suke yin amfani da ita mai kamshi suna sha ko don bakin nasu zai daina wari amma kuma baya dainawa.
To kusani cewa akwai amosani a baki kamar yadda akwai amosani a kunne, ido da kuma amosani na kai. To shima baki yana da wannan amosanin. Masana wanda suka san ciwo da amosani irin na baki sunce wani lokacin amosanin dake kan mutum shine yake saukowa ya tawo ido sannan kuma daga ido ya tawo baki.
To hakan ke jawo kaji mutum bakinsa kusan koda yaushe yana wari duk kuwa da irin wanke shi da yake yi, musamman a wannan lokacin da muke ciki na watan Ramadan wanda mutum yake dadewa bai ci abinci ko yasha wani abin sha ba.
Sai kaji idan mutum ya bude baki ko idan yai magana sai kaji kamar an bude masai saboda tsabar wari, duk da dai munsan cewa warin bakin mai yin azumi ibada ne, inda Annabi (SAW) yake cewa warin bakin mai yin azumi kamar turaren miski ne a aljanna.
Amma dai duk da haka saboda mutum ya fita hakkin mutane domin kana cudanya da mutane za kaje wajen Sallah ko wajen karatu ko kuma wajen hira kaga dole idan kayi magana aji wari, sannan kuma idan kana da iyali dole ai zaka kusance su. To kaga dai wannan duk shiga hakki ne wanda ya kamata mutum ya dauki mataki.
Don haka idan mutum yana fama da wannan matsala ta warin baki ga wasu abubuwa 2 da nazo muku dasu da za ku yi amfani dasu domin ku samu waraka.
Idan mutum yai sahur yasha ruwa kafin ayi kiran sallah za ka samu kwayoyin kaninfari kamar 3 kasa a bakin ka kana tsotsa kana yin wasa dasu, za kaji zafi a haka za kai ta wasa dasu a bakin ka har tsawon kamar minti 10.
Idan kayi haka sai ka zubar dasu sannan ka samu zuma kamar cokali 1 ka sha. Haka zaka dinga yi a kullum.
Haka kuma idan bayan mutum yasha ruwa ma'ana idan ya kai azumi sai ka samu Kaninfari guda 3 ka saka a bakin ka shima kai ta wasa dasu har zafin ya dushe sai ka watsar dasu sai ka dauki zuma kasha.
Haka zaka dinga yi a kullum sau 2 to Insha Allah indai matsala ce ta warin baki da wannan amosanin da yake tattaruwa a harshe da hakora za'a neme shi a rasa domin zai fitar da dukkan wani datti ko kuma wasu abubuwa da suke jawo wannan warin bakin.