Yadda Zaku Haɗa Sabulun Gayran Jiki Da Kanku |
Wasu na yawan cewa munfi kawo abubuwa game da mata fiye da maza. Ku sani cewa mata sune kan gaba idan suka gyaru al'umma ta gyaru idan kuma suka ɓaci al'umma ta lalace. Shiyasa muke yin iyakacin ƙoƙarin mu domin ganin mun kimtsa su mu daidaita musu sahu shi muke yi wajen ganin sun gyara jikin su sun tsaftace shi.
Mata munsha faɗa muku cewa ba kowane irin abu ne zaki ringa yin amfani dashi ba wajen gyaran jikin ki ko fuska ko kuma makamancin haka. Domin idan kinayin hakan watarana zaki haifarwa da kanki matsala maimakon a samu nasara sai kuma matsala ta faru. Musamman mata masu goga abubuwa a fuska domin samun haske da kyan fuskar, dole ku kiyaye da abinda zaku ringa shafawa don gudun matsala.
Shiyasa yau ma nazo muku da wani sabulu da zaki haɗa da kanki ki ringa yin amfani dashi domin zai taimaka miki wajen gyara miki fatar jikin ki tare da sa fatar ta yi kyau ta yi haske. Shi wannan sabulun wanka zaku ringa yi dashi, kuma shi wannan sabulun har maza ma suna iya haɗawa su yi amfani dashi ba iya mata ba. Kaima namiji idan kana so fatar jikin ka ta gyaru ka haɗa ka ringa yin wanka dashi.
Yadda Zaku Haɗa Sabulun Gayran Jiki Da Kanku
Uwargida ko amarya idan zaku haɗa wannan sabulun kuyi shi mai yawa yadda zaku daɗe kuna amfani dashi tare da maigida. Abubuwa 4 ne zaku nema idan zaku haɗa wannan sabulun. Amma ku tabbatar duk kun same su domin ko abu guda ne baku yi amfani dashi ba to haɗin ba zaiyi muku aiki ba. Ga abubuwan da zaku nema kamar haka;
(1) Man Kaɗanya
(2) Man riɗi, ana kuma kiransa da 'simsim'
(3) Sabulun Salo, wasu sunfi kiransa da sabulun Ghana, amma dai a ƙasar yarabawa ake yin sa.
(4) Man Zaitun.
Waɗannan Abubuwan su zaki haɗa ki zuba a tukunya ki dafa su su narke, sai ki zuba gashiri rabin ƙaramin cokali, amma kada ki zuba ruwa. Kawai iya abubuwan da muka lissafa 4 su zaki haɗa ki dafa su. Idan sun dafu sai ki sauke ki juya sosai yadda zasu haɗe jikin su. Zaki barshi ya huce na tsawon kamar awanni 4 idan ya bushe zakiga ya daskare.
Zaki ringa yin wanka dashi koda yaushe, idan kuma iya fuska kikeso zaki ringa wanke fuksa, ba sai duka jikin ba. Amma dai anaso a ringa wanke jiki gabaki ɗaya dashi saboda ke kanki kinaso kiga dukkan jikin ki ya yi haske yai kyau. Zakuga yadda fatar jikin ku za ta yi kyau tayi laushi.
Idan zaki amfani dashi zaki fara shafawa a wajen da kikeso ko jiki ko kuma fuska sai ki bari yai kamar minti 20 sannan sai ki wanke. Idan kinayin hakan to wallahi za kiga jikin ki ya canja sosai, kuma ba zaki ƙara neman wani sabulu ko wani mai ba wannan ya wadatar. Idan kun haɗa ku sanarwa da sauran ƙawayen ku da ƴan uwa domin suma su yi. Allah ya haɗa mu a ladan.