Yadda Za Ku Kare Kanku Daga Shaiɗanun Aljanu |
Barknmu da wannan lokacin barkanmu da sake saduwa da ku a filin shirye-shiryen da muke kawo muku. Kamar kullum yau ma cikin yardar Allah na kawo muku wata fa'ida wacce duk wanda yai amfani da ita Insha Allah zai samu kariya da waraka daga shaiɗanun aljanu.
Ga dukkan masu fama da matsalolin aljanu a gida ko wajen aiki ko dukkan wani waje da ake zama ko kuma wanda ake aikawa ko kuma suke buge mutane suka addabe ku to insha Allah idan kun yi amfani da wannan hanyar da za mu baku to za ku samu waraka cikin ƙaramin lokaci da izinin Allah.
Yadda Za Ku Kare Kanku Daga Shaiɗanun Aljanu A Gidajen Ku Da Dukkan Wajen Sana'ar Ku
Akwai mutane wanda zama a gidan su ma gagarar su yake yi saboda matsalolin aljanu da suke addabar su a gidan na su. Sai kaga sun kasa ɗaukar mataki akan wannan matsalar, shi yasa a yau muka wata hanya mai sauƙi na yadda za ku kare kanku daga dukkan wani sharri na shaiɗanun aljanu.
Don haka ga duk wanda suke son su yi maganin irin wannan matsala ta sahiɗanun aljanu akwai abubuwan da ake so ku nema domin da su ne za kuyi wannan haɗin maganin. Ga jerin abubuwan da za ku nema kamar haka;
(1) Man Gelo wanda a turance ake kira da (castor oil)
(2) Jan Miski wanda da turancin ake kiran sa (red musk)
Wannan abubuwa guda biyu sune za ku nema, amma ku tabbatar an baku masu kyau, kuce a baku na gida domin sun fi kyau shi man gelo ɗin za kuji yana da wari sosai. To shi zaku siya. Shi kuma Miski ɗin kuce a baku wanda yake jajur ne. Idan kun same su sai ku haɗe su waje guda amma anfi so man gelo ɗin yafi yawa.
Bayan kun haɗe su waje ɗaya sai ku zuba a kwalba ku tabbatar da kwalbar a buɗe take sai ku ɗora akan taga wato window ko kuma a wani waje daban kamar ƙofar gida ko tsakar gida ko ƙofar ɗaki har cikin ɗakin ma kuna iya ajiyewa babu matsala.
Idan ku kayi hakan to insha Allah kowane irin shaiɗani ne yake damun ku to zai bar gidan ba zai kara shigowa ba. Domin wasu mutanen suna da sakaci a irin wannan yanayin amma saboda rashin kulawa da kuma mayar da hankali sai abun ya citura sai kaga ana neman yadda za'a yi.
Don haka duk wanda yaji wannan fa'idar kan yadda za ku kare kanku daga Shaiɗanun aljanu to yayi ƙoƙarin yin amfani da ita, kuma ko bakada shaiɗanu a gidan ka zaka iya yi domin kariya ne. Kuma zaka iya samarwa da sauran al'umma suma suyi amfani da wannan fa'idar.
Da fatan za kuyi ƙoƙarin yin wannan haɗin kuma a sanar da sauran ƴan uwa domin su ma su yi amfani dashi. Muna addu'ar Allah ya tsare mu daga sharrin shaiɗanu a duk inda suke, kuma muna addu'ar Allah ya kare gidajen mu da duk inda muke yin sana'ar mu.
Tags:
Daga Malamai