Labaran Duniya
Yadda Wasu Mayaƙa Da Ake Zaton Ƴan Fashin Daji Ne Suka Hallaka Ƴan Sanda Biyu A Jihar Katsina
Monday, January 20, 2025
0
Yadda Yan Bindiga Suka Hallaka 'Yan Sanda Biyu A Katsina |
Wani rahoto daga Jihar Katsina ya tabbatar da cewa wasu jami'an tsaro na yan sanda su biyu sun rasa rayukansu a yayin wani artabun da suka yi da ƴan bindiga.
Cp Sunusi wanda shine Kwamishinan ƴan sanda a jihar ta Katsina shine ya tabbatar da faruwar al'amarin a lokacin da yake ganawa da manema labarai a babban ofishin ƴan sanda dake birnin jihar ta Katsina.
Cp Sunusi ya ce ASP Zaharadden Yuguda da Yakubu Joshua sune yan sandan da aka kashe a yammacin ranar Alhamis a yayin da suke yin artabu da yan fashin daji masu satar mutane. Haƙiƙa munyi baƙin cikin rashin waɗannan jami'an namu guda biyu da ƴan fashin dajin suka kashe su.
Wata majiya dai ta bayyana cewa artabun da aka yi tsakanin an bindigar da jami'an ƴan sandan ya faru ne a kauyen Baure na ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina. Ance an ɗauki tsawon lokaci ana musayar wuta a tsakani wanda kuma daga ƙarshe dai yan fashin dajin suka hallaka biyu daga cikin jami'an ƴan sandan.
Bayan faruwar lamarin ne sai Kwamishinan ƴan sanda ya bada umarni ga wata tawaga ƙarƙashin jagorancin mataimakin sa wanda ke kula da shiyyar Dutsinma wato ACP Aminu Umar zuwa inda ƴan fashin dajin suke a ɓoye domin kai musu hari tare da tabbatar da sun yi nasarar kame su ko kuma hallaka su.
Ance bayan yin musayar wuta ne ƴan sandan suka yi nasarar kashe ƴan fashin dajin su biyu yayin da sauran suka gudu suka bar makaman su masu tarin yawa ciki har da bindigogi ƙirar AK 47 da yawa da kuma tarin alburusai.
Kwamishinan ya nemi al'umma mazauna yankunan da maƙobta akan su cigaba da zuba ido ga irin motsin al'umma Wanda basu yarda dasu ba kuma su yi ƙoƙarin kai rahoto ga jami'an tsaro domin ɗaukar mataki. Sannan kuma yace za su cigaba da yin ƙoƙarin su wajen yaƙar ƴan fashin dajin.
Jihar Katsina dai ta ɗauki tsawon lokaci tana fama da matsalolin tsaro na ƴan fashin daji musamman Masu yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa wanda har yakai ga suna shiga makarantu suna tafiya da ɗalibai domin su nemi kuɗin fansa.
Sai dai kuma gwamnati tace tana yin iyaka ƙoƙarin ta wajen ganin ta kawo karshen ƴan bindigar a fadin Jihar baki ɗaya. Sai dai kuma duk da irin wannan furucin da gwamnati ta daɗe tana yi har yanzu dai ba'a daina aikata abubuwan da ake yi ba wanda masana harkokin tsaro ke ɗaura laifin akan gwamnati.
Yanzu dai abin jira agani shine ko za'a magance wannan matsalar da taƙi ƙarewa a jihar Katsina da sauran jihohin Zamfara da Sokoto wanda su ma suna fuskantar matsalolin ƴan fashin dajin.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment