Yadda Mayaƙan ISWAP Suka Sa Manoma Da Mazauna Biyan Haraji A Sassan Yankuna A Jihar Borno - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Yadda Mayaƙan ISWAP Suka Sa Manoma Da Mazauna Biyan Haraji A Sassan Yankuna A Jihar Borno

Yadda Mayaƙan ISWAP Suka Sa Manoma Da Mazauna Biyan Haraji A Sassan Yankuna A Jihar Borno
Yadda Mayaƙan ISWAP Suka Sa Manoma Da Mazauna Biyan Haraji A Sassan Yankuna A Jihar Borno



Manoma da makiyaya mazauna garin Damboa a jihar sun fara biyan haraji ga ƙungiyar mayaƙan ISWAP dake jihadi a yammacin Afrika.


Rahoto ya bayyana wani jami'in gwamnati shine ya bayyana wa manema labarai irin halin da manoma suka tsinci kansu a ciki inda yace yanzu manoma suna ƙarƙashin ikon ƴan ta'addan ISWAP a yankin Damboa na jihar ta Borno. Yace mayaƙan sun baiwa mazauna garin damar noma gonakin su sannan kuma za su ringa karɓar haraji a matsayin Zakka daga wajen kowane manomi idan ya girbe amfanin gonar sa.

Wata majiya ta rawaito cewa manoman sun karbi wannan tsarin da ISWAP ɗin tai musu domin hakan sauƙi ne a gare su. Domin idan ba su yi ba to ba za su samu damar yin noman ba, kuma idan ba su yi noman ba, babu yadda za ayi su ciyar da kan su don haka ne suke ganin dole su bi umarnin da Mayaƙan suka ba su na biyan haraji.

 

Ko a lokacin da ƙungiyar Boko Haram suke ƙarƙashin jagorancin Abubakar Sheƙau ba sa barin jama'a su yi noma wanda kuma hakan ke jawo musu rashin samun abinci, amma yanzu bayan da ƴan ISWAP suka yi juyin mulki su sun amince ayi noma amma sai an biya haraji da kuma bayar da zakka.


Wani manomi mai suna Mrusha, ya shaidawa wani gidan jarida cewa manoman ba su san cewa mahukunta sun san halin da suke ciki ba. Yace ko a shekarun baya sai da mayaƙan Boko Haram da dama suka kashe manoma masu yawan gaske a lokacin da suke girbe kayan amfanin gonar su da suka noma. Sai dai kuma a wannan lokacin hakan ba ya faruwa idan har an biya haraji.


A farkon wannan ne suka same ni a cikin gona inda suka shaidamin cewa idan lokacin girbi ya zo to za mu ba su nasu kason, amma ba yadda na iya dole haka nace na amince da sharaɗin na su. Idan nace ban amince ba to za su iya cutar dani kuma babu damar zuwa gonar.


Ance kawo yanzu dai Mayaƙan na ISWAP sun kafa tushe mai ƙarfin gaske a arewa maso yammacin Borno inda suke cin karen su babu babbaka, a baya bayan nan sun fara yaɗuwa a kudancin jihar ta Borno wanda suke karɓar kuɗaɗen haraji daga hannun mazauna gari da direbobi da monama a yankunan.


A cikin wannan shekarun ne dai manoma musamman mazauna ƙauyuka a jihohin Borno, Adamawa da yobe suna fuskantar ƙalubalen ƴan ta'adda baya ga kai hare-hare, ga kuma saka haraji wanda wani salo ne na karɓar kuɗi da kayan abinci daga hannun al'umma.


Wannan ne ya jawo al'umma ke mamakin irin yadda gwamnati ta zuba ido ta na kallon irin wannan cin kashi da ƴan bindigar suke yi amma ba ta ɗauki mataki ba. Sai dai ita gwamnatin tana cewa tana yin iya ƙoƙarin ta wajen ganin ta kawo karshen matsalar. Amma mutane suna jinjinawa gwamna Babagana Umara Zulum, ganin cewa tun da yazo kan mulki yake ƙoƙarin daƙile ayyukan mayaƙan.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel