Yadda Jinin Haila Yake Da Yadda Ake Bambance Shi Da Jinin Cuta |
Wani lokacin jini ya kan yankewa mace kuma ta kasa gane cewa ko jinin Haila ne ko kuma jinin cuta wato istihadha. Wannan ya kan rikita musu lissafi wajen gudanar da ibada da kuma sanin matsayin lafiyarsu.
Yadda Ake Bambance Jinin Haila Da Na Cuta
1- Jinin Haila ruwan kasa ne, ba ja ne sosai ba, shi kuma jinin cuta za ki gan shi ja ne sosai kamar jinin ciwo.
2- Jinin Haila yana dan yin wari, za ki ji yana dan wani wari mara dadi amma jinin cuta ba ya wari.
3- Jinin Haila yana fitowa ne da karfi, ma'ana za ki ji kamar ana turo shi ne amma shi jinin cuta a slow yake fita, ba da karfi ba.
4- Jinin Haila ya kan zo da lalura kamar ciwon mara, ciwon kafa da dai sauransu, shi kuma jinin cuta bai fiye zuwa da lalura ba, sai dai wani lokaci ya kan zo da ciwon mara.
5- Jinin Haila yana da kauri sosai, shi kuma jinin cuta ba shi da kauri.
6- Jinin Haila ba ya bushewa, idan ya diga a kasa za ki ga ya ki bushewa amma shi jinin cuta nan da nan yake bushewa.
7- Za ki ga jinin Haila yana kyalli, yana sheki, shi kuma jinin cuta ba shi da kyalli.
8- Idan mace ta kasa bambance jinin da ya zo mata ta wadannan alamomi, to sai ta samu babbar roba ko bahon wanka, ta zuba ruwa a ciki, ta shiga ciki ta zauna. Idan ta ga yalo ya taso sama to jinin cuta ne amma idan ba ta ga yalo ba to jinin Haila ne.
Idan kaji kunyar yin tambaya gameda yadda zaka gudanar da ibadar ka ka zauna cikin duhu da jahilci to ka sani/ ki sani wutar jahannama bazata ji kunyar konakaba.
Sai dai kowacce tambaya ana yintane a inda yadace, ina fata anfahimta?
wallahu aalamu
Allah ya ƙara mana shiriya gaba dayanmu ya wadata mu da ilimi mai amfani