Yadda Ake Addu'ar saduwa da iyali |
Annabi (S.A.W) yace: “Da ɗaya daga cikinku lokacin da zaije wa iyalinsa ya ce: Ya Ubangijina ka nesantar da shaiɗan daga garemu, haka nan ka nesantar da shaiɗan daga abinda ka azurta mu dashi. Idan har Allah ya hukunta samun ɗa a tsaƙaninsu ta wannan saduwa da sukayi shaiɗan ba zai cutar dashi ba.”
Yadda Ake Addu'ar saduwa da iyali
Akwai ma'aurata da yawa da basu damu da yin addu'a ba a yayin kwanciyar jima'i da iyalansu ba, hakan yasa muka kawo muku yadda ake yi domin ma'aurata su amfana.
Addu’ar itace:
Allahumma Jannib na-sshaiɗana wa jannibi-sshaiɗana ma Razaqtana.
Yana da kyau Mu kiyaye wannan addu’a, domin yana da matuƙar Mahimmanci, hakanan Wanda zaiyi wannan addu’a yayin saduwa shine Miji.
Wannan shine bayani kan yadda ake addu'ar saduwa da iyali da fatan Allah yasa mudace, ya kuma bamu kariya.