Wasu Mutane Sun Shiga Gidan Wata Mata Sun Kashe Ta A Unguwar Ɗanbare Ta Jihar Kano - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Wasu Mutane Sun Shiga Gidan Wata Mata Sun Kashe Ta A Unguwar Ɗanbare Ta Jihar Kano

Wasu Mutane Sun Shiga Gidan Wata Mata Sun Kashe Ta A Unguwar Ɗanbare Ta Jihar Kano
Wasu Mutane Sun Shiga Gidan Wata Mata Sun Kashe Ta A Unguwar Ɗanbare Ta Jihar Kano


Wasu mutane da har kawo zuwa wannan lokacin ba'a san ko suwaye ba sun shiga gidan wata matar aure mai suna Ruƙayya Mustapha sun kashe ta tare da raunata yaran ta ƙanana guda 2 a unguwar Ɗanbare dake yankin karamar hukumar Gwale a jihar Kano.


Wata majiya ta sanar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, inda ake tunanin cewa wanda suka kashe Ruƙayya sun shiga gidan ne da rana suka hallaka ta, bayan haka kuma akwai yaran ta ƙanan su biyu su ma sun raunata su.


Sai dai bayan duba jikin marigayiyar babu wasu alamu dake nuna cewa yankata akai, sai dai ana tunanin cewa sun yi amfani da taɓarya ne suka buga mata akan ta wanda zafin buguwar yasa ta mutu nan take.


Kawo yanzu dai ba'a san taƙamaiman abinda ya faru a gidan ba, sai dai akwai wasu masu yin aikin gini da suke maƙota da gidan Ruƙayya. Sai dai jami'an tsaro sun Kama su domin gudanar da bincike akan su.


Tun bayan faruwar lamarin babu wanda yasan hakn ta faru har sai da maigidan ta ya dawo daga kasuwa inda ya riske matar tasa a kwance a ƙasa babu rai. Rundunar ƴan sandan jihar Kano tace ta kame mutane 5 da ake zargin su da hannu a kisan na Ruƙayya.


A yayin ziyarar ta'aziyya da mataimakin gwamna ya kaiwa iyalan Ruƙayya ya bayyana cewa sun ji takaicin kisan da akaiwa Ruƙayya, kuma gwamanti za ta ɗauki dukkan matakan da yakamata domin kamo wanda suka aikata laifin.


Unguwar Ɗanbare dai ana yawan samun matsaloli na rashin tsaro kuma ana yawan samun labarin irin yadda ake bayar da gidajen haya babu tsari ga kuma mata masu zaman kansu da sukai yawa a unguwar.


Sai dai ƙungiyar sa kai ta unguwar suna iya ƙoƙarin su wajen ganin sun magance matsalolin da suka addabi yankin.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel