Wannan Sune Abubuwan Da Suke Hana Mata Samun Rahama Da Dacewa A Wajen Allah A Ranar Al-Ƙiyama - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Wannan Sune Abubuwan Da Suke Hana Mata Samun Rahama Da Dacewa A Wajen Allah A Ranar Al-Ƙiyama

Wannan Sune Abubuwan Da Suke Hana Mata Samun Rahama Da Dacewa A Wajen Allah A Ranar Al-Ƙiyama
Wannan Sune Abubuwan Da Suke Hana Mata Samun Rahama Da Dacewa A Wajen Allah A Ranar Al-Ƙiyama



Barknmu da sake saduwa da ku a wannan lokacin a cigaba da shirye-shiryen da muke kawo muku daga fatawoyin malamai.


A cikin wannan rundun na yau za kuji wasu jerin abubuwan da suke jefa mata zuwa ga halaka su hana su samun rahamar Allah SWT. Sai dai kuma waɗannan abubuwan da yawan mata ba sa dauƙar su da muhimmanci. Shi yasa a yau muka shirya kawo muku su domin tunatar da iyayen mu mata don su gyara kuma su kiyaye. Da fatan fatan za'a yi amfani da wannan abubuwan da zamu tunatar da ku, kuma ku kiyaye.


A cikin wannan rubutun na yau zaku ji jerin wasu abubuwa wanda suke jefa mata ga halaka su hana su samun rahama daga Allah. Sai dai kuma wannan abubuwan ba'a ɗaukar su da muhimmanci. Shine yasa a wannan rubutun muka shirya yi muku rubutu akai domin tunasar da ƴan uwan mu mata domin su gyara kuma su kiyaye. Da fatan za'a yi amfani da abubuwan da zaku karanta.


Abubuwan dai suna da yawa amma a wannan lokacin dai za mu kawo muku wasu kaɗan daga cikin su. Anan gaba kuma Insha Allah za mu kawo muku ƙarin wasu. Ga dai jerin abubuwan Kamar haka:


(1)  Matar Auren Da Ya Yi Zina;

Duk matar da take da aure ta yi zina da wani namiji wanda ba mijin ta ba to babu shakka babu ita babu samun rahamar Allah. Irin hakan kuwa a yanzu ya zama ruwan dare, mata suna fita daga gidajen su da nufin za su je unguwa amma kuma ba haka bane sun yawo ne wajen wasu kazan banza suna yin zina da su. Don haka idan kinsan cewa kina irin wannan dabi'a to kuyi gaggawar tuba kuma kidaina.


(2) Mace Da Ya Mallake Mijinta Ta Hanyar Asiri;

Duk macen da ta mallake mijinta ta hanyar yin siddabru, tsafi ko asiri a wajen malamai ko kuma boka to tana tare da fushin Allah. Abinda zai baka mamaki shine a yanzu sai kaga mace taƙi yin abubuwan da za su jawo hankalin mijin ta irin na soyayya da kulawa da shi da nuna masa soyayya duk ba za ta yi ba sai dai kawai taje wajen bokaye su yi mata asiri akan mijin na ta.


(3) Macen Da Ta Hana Kishiyar Ta Zaman Lafiya Da Mijin Ta;

Mata da yawa idan mijin su ya ƙaro musu Kishiya sai kaga babu zaman lafiya, ita uwar gidan duk sai ta tada hankalin ta har ta yi ƙoƙarin raba amaryar da mijin na ta, ko kuma tai masa asiri yaji cewa ya tsani amaryar. To Uwagida kisani cewa wannan babban laifi ne kuma idan baki tuba kin daina ba ba zaki samu rahamar Allah ba.


(4) Macen Da Ta Raba Mijinta Da Iyayen Sa Da Ƴan Uwansa;

Duk Macen da ta raba mijinta da Iyayen Sa da kuma ƴan uwansa ta hanyar yin asiri ko kuma wani siddabru, domin akwai matan da zakiga suna jin haushin iyayen sa da kuma ƴan uwansa ba sa son ya raɓe su sai su yi masa asiri ko wani tsafi da zaiji cewa ya tsane su. To wallahi kisani cewa Allah ba zai rabu dake ba kuma ba zaki samu abinda kikeso ba.


(5) Macen Da Ta Yi Cikin Shege Daga Waje Ta kawo Gidan Miijin Ta;

Wani zamani ya zo da za kaga matan aure ba su ɗauki zina da komai ba, kuma a irin hakan ne sai kaga wasu sun je suna yawon banza har kuma su yi ciki su kawo gidan mijin su. To Allah ya tsinewa duk irin matan da suke irin wannan dabi'a, kuma tun a duniya za kuga sakamakon abinda kikayi.


Wannan sune kaɗan daga cikin abubuwan da za mu iya kawo muku a halin yanzu wanda suke jefa mata ga halaka kuma ba za su samu rahamar Allah ba.  Kuma kamar yadda na faɗa muku abubuwan suna da yawan gaske amma a yanzu ba zamu iya kawo muku su ba.


Don haka ne dole ne mata ku kula a san irin zaman da za'a ringa yi da mazajen ku, domin duk irin wannan laifukan da muka lissafa duk wacce take aikata su to wallahi ba za ta samu rahamar Allah ba. Kuma kisan cewa idan kika cuce shi to kanki kika yiwa kuma Allah ba zai ƙyakeki ba tun daga duniya sai kinga sakamakon Abubuwan da kikayi kafin ake lahira.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel