Wannan Haɗin Na Maza Ne Ana Yin Amfani Dashi Minti 30 Kafin Mutum Ya Kwanta Da Iyalinsa |
Banda mara mata, idan kasan ba kada mata kaje ka haɗa to babu ruwana kuma kai da Allah. Ka bari idan ka yi aure sai kaje ka haɗa amma ba yanzu ba. Domin za mu bada wannan fa'ida ne kawai ga masu aure banda marasa aure.
Wannan haɗin na ma'aurata ne shiyasa tun farko mukace banda marasa aure. Kuma shi wannan haɗin da za mu baku ingantacce ne domin mutane da yawa sun haɗa sun yi amfani dashi kuma sun ji daɗin sa. Shiyasa muka shirya kawo muku shi domin wanda basu sani ba su sani kuma su gwada.
Shi dai wannan haɗin ba shi da wahalar haɗawa abubuwan da za'a nema abu biyu ne kacal.
(1) Citta, ɗanya mai yatsu
(2) Lemon Tsami
(3) Zuma (Honey)
Idan an samu waɗannan abubuwan da muka ambata, ita cittar guda ɗaya ta isa. Sai ku samu turmi ku jajjaga wannan cittar ku zuba ta a cikin tukunya, sai ku ɗauko lemon tsami ku raba shi gida huɗu ku matse a cikin wannan cittar sai a zuba ruwa kamar kofi ɗaya abar shi ya tafasa.
Idan ya tafasa sai a sauke a barshi ya ɗan sha iska sannan sai ku ɗauko zuma ku zuba kamar cokali biyar a juya. Ba za'a sha wannan haɗin ba sai ya rage kamar minti 20 a fara kusantar Iyali sannan sai a sha. Ba sai na ƙara wani dogon bayani ba. Idan kun yi za kuji abinda wannan haɗin zai muku.
Kada ku yi sake dashi. Idan kun haɗa kunji daɗin sa sai ku yi mana addu'a sannan kuma ku turawa sauran ƴan domin su ma su amfana daga wannan fa'ida. Muna fatan Allah ya haɗamu a ladan gabaki ɗaya Amin.