Haɗin matan aure |
Mata iyayen mu kuma iyayen gida, tilas ne mu ringa kawo muku abubuwan da za ku ringa gyara jikin ku. Yau ma gashi mun kawo muku wata tsaraba. Wannan wani taimako ne da muka zo muku dashi domin kuyi amfani dashi ku gyara jikin ku, sai dai ba zai yi miki aiki ba sai idan kina cikin damuwa ko kuma idan hankalin ki yana tashi ko idan kin saka damuwa a ranki don haka dole mata ku kwantar da hankalin ku.
Maganar gyaran nono, nono ya lalace nono ya zube, nono ya tamushe, haka idan kika duba jikin ki za ki samu shima ya tsofe ya tamushe saboda babu kwanciyar hankali. Kuma abubuwan da akace ku ringa ci kuna sha bakwa yin amfani dasu kuma ba tsada ne da su ba. Kayan marmari irin su kankana, lemo, ayaba, kwakwa dabino. Ganye irin su zogale alayyahu, rama, yaɗiya duk bakwa amfani dasu. Shiyasa zaka ga wasu matan suna cikin mawuyacin hali.
Wasu matan kuma akwai hali na siyan dukkan wani abinci mai gina jiki amma saboda ba su da kwanciyar hankali a tare dasu. Sai su yi ta neman maganin nono, na gargajiya ko kuma na bature. Kuma yawancin irin maganin da kuke amfani dashi ba'a samun biyan buƙata. Wasu maganin ma sai dai su ƙara lalata nono ko kuma su ƙara jawo wata matsalar. Shiyasa muke kawo muku maganin da zaku haɗa da kan ku.
Wannan Haɗin Na Matan Da Suke Shirin Yin Aure Ne Bayan Azumi
Ga wani abu da zan baku amma shi wannan na shafawa ne, idan kin haɗa zaki ringa shafa shi a nonon ki idan kin shafa sai ki saka rigar nono zaki barshi yai kamar awa 3 yana jikin ki daga bisani sai ki cire rigar nono ki wanke maganin da kika shafa. Mata da yawa sun yi wannan haɗin kuma sun ji daɗin sa yayi musu aiki sosai, don haka kuma sai ku yi amfani dashi.
Zaki samu kokomba (cucumber) sai ki samu wannan ƙarfen da kuke gurje Kuɓewa dashi ku gurje kokomba. Idan bakuda ƙarfen sai ku yayyanka ku daka. Sai ki samu ƙwai ɗanye ki fasa ki zubar da farin ruwan, ƙwanduwar dita ake da buƙata. Sai kije chemist wajen masu sayar da magani kice a baki vitamin E zakiga yana kama da ja da yalo sai sai shi ruwa ne a cikin sa.
Sai ki ɗauki guda 1 ki zuba a cikin wannan haɗin na kokomba da ƙwai ki juya shi sosai sai ki ringa ɗiba kina shafawa akan nonon ki gabaki ɗaya idan kin shafa sai ki ɗauki rigar nono ki rufe shi ki barshi har tsawon awanni 3 sai ki wanke. Haka zaki da safe da yamma haka zaki. Zaki iya haɗa na kwana 3 amma ki ringa ajiye shi a waje mai sanyi yadda ba zai lalace ba. kullum haka zaki har zuwa tsawon wata 1. Zakiga yadda nononki zai gyaru.