WACE KULAWA MAI FAMA DA YOYON FITSARI YA KAMATA TA SAMU? - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

WACE KULAWA MAI FAMA DA YOYON FITSARI YA KAMATA TA SAMU?

WACE KULAWA MAI FAMA DA YOYON FITSARI YA KAMATA TA SAMU?
WACE KULAWA MAI FAMA DA YOYON FITSARI YA KAMATA TA SAMU? 


Yoyon fitsari abune mai ciwo ga wanda ya kamu dashi domin kuwa indai ba makusantaba suma masoya na gaske,sai ma'aikatan asibiti sune kadai suke iya zuwa kusa da mutum suyi mu'amala dashi kamar sauran mutane.


- Kulawa ta farko shine ayi qoqarin yin tiyata domin gyara wurin da ya huje.


-Tsaftace muhallin su da kayan da suke amfani dasu saboda a samu sauqin mu'amala dasu.


-Kula da robar fitsarin da aka saka musu akai-akai (catheter) da zubar da fitsarin da ya taru cikin jakar da suke dauke da ita (Urine bag) gudun kar su kamu da wani ciwon daban.


-Kula da jikin su ta hanyar yin wanka da canja kaya domin inganta lafiyar su.


-Tabbatar da cewa basa zama cikin danshi saboda kiyaye su daga larurar zagwanyewar fata (Skin ulcer /Pressure Sore).


-Samar musu da abinchi mai gina jiki dazai taimaka musu wurin saurin warkewar ciwon jikinsu.


-Tsaftace wurin da yake fitar da fitsari akai-akai.


-Kula da basu magunguna bisa qa'ida.


-Qauracewa tsangwamar su ko qyama a garesu domin lafiyar tunanin su.


-Da sauran su 


Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad 

RN,RM,PND 


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel