Volkswagen Beetle mota mafi shahara a tarihi — Android Pols
![]() |
Volkswagen Beetle mota mafi shahara a tarihi |
The Volkswagen Beetle, wata karamar mota ce ta iyali da kamfanin Jamus Volkswagen ya kera daga 1938 zuwa 2003. Daya ce daga cikin manyan motocin da suka shahara a tarihin kera motoci. Shekaru 65 kamfanin yana fitar da samfurin motar, shi ne lokaci mafi tsayi a cikin ƙarni na kera mota samfuri iri ɗaya. An kera motar sama da miliyan 21 da dubu 500, ita ce samfurin mota mafi yawa da aka taba kerawa a tarihi.
A cikin watan Mayu 1934, a wani taro a Kaiserhof Hotel na birnin Berlin, shugaban Jamus hitla ya dage kan samar da abin hawa wanda zai iya ɗaukar manyan mutane biyu da yara uku, kuma ka da tayi amfani da fiye da lita bakwai na man fetur a kowace tafiyar kilomita 100. Kuma an tsara ta don kada tayi tsada, saboda talakawa masu karamin karfi su mallaka.
A ranar 22 ga Yuni 1934, Ferdinand Porsche ya karɓi kwangilar kera motar daga Verband der Automobilindustrie (Ƙungiyar Masana'antun kera Motoci ta Jamus) don kera motar fasinja mara tsada, bayan Hitila ya yanke shawarar cewa akwai buƙatar ta zama motar jama'a mai araha wacce za ta isa ga masu karamin karfi su mallaka.
Leave Comments
Post a Comment