Ƙungiyar Tace Fina-Finai Ta MOPAN Ta Ja kunnen Ƴan Ƙannywood A Kan Su Daina Tonawa Kan Su Asiri
Ƙungiyar Tace Fina-Finai Ta MOPAN Ta Ja kunnen Ƴan Ƙannywood A Kan Su Daina Tonawa Kan Su Asiri |
Ƙungiyar tace finafinai ta arewacin Najeriya da ake kira da MOPPAN, ta yi kira da kuma jan kunne ga ƴan ƙungiyar Kannyowood da su daina fitowa shafukan sada zumunta suna tonawa kansu asiri. MOPPAN ɗin ta ce abinda ke faruwar a masana'antar ba abune mai daɗi ba.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta MOPPAN ta fitar wacce ta baiwa gidan Jaridar BBC Hausa, sun ce abinda ke faruwa a Ƙannywood ɗin cin mutuncin juna ne bai kamata su ringa aikata hakan ba a bainar jama'a.
Al-amin Ciroma wanda shine mai magana da yawun ƙungiyar ta MOPPAN ya ce munga abubuwan da suka ringa faruwa na cin mutuncin juna wanda ba muji daɗin hakan ba. Ai bai Kamata ku fito kafafan sadarwa kuna maida maganganu ga junan ku ba, haka ya nuna rashin haɗin kai da kuma shugabanci a masana'antar, a cewar sa.
Sannan kuma ya kara da cewa sun samu saƙonni daga ƙungiyoyi da kuma ɗaiɗaikun mutane da yawa da suka rubuto musu wasiƙa kan cewa su tsawatar akan abinda ke faruwa a Ƙannywood, wanda hakan yasa muka fito muke kira a gare su da su yi ƙoƙari su daidaita tsakanin su. Kuma su nemi yafiyar junan su.
Dr Ahmad Muhammad Sarari wanda shine shugaban ƙungiyar MOPPAN ta kasa yace sanin muhimmanci kiraye-kirayen da ƙungiyoyi da al'umma suke yi yasa muka ɗauki ƙwararan matakai tare da haɗin gwiwar sauran ƙungiyoyi kamar irin su ƙungiyar masu shirya film ta arewa wato AFMAN.
Rikicin dai na Kannywood ya samo asali ne tun bayan wata hira da akai da wata tsohuwa da ta daɗe tana fitowa a fina-finai inda a hirar ta bayyana cewa ta shafe shekaru 50 tana yin sana'ar amma babu wanda ya taɓa biyan ta sama da dubu 5 idan an saka ta a film.
Wanda hakan ya jawo wasu daga cikin masana'antar suka dinga karyata kalaman da tsohuwar ta yi, inda wasu kuma ke kare ta. Daga cikin masu kare ta akwai Naziru Sarkin Waƙa wanda ya gaskata abinda tsohuwar ta faɗa inda kuma daga bisani ma ya bata kyautar kuɗi miliyan 2 domin ta yi sana'a.
Leave Comments
Post a Comment