Ƙungiyar Matan Kannywood Sun Baiwa Sarkin Waƙa Kwana 3 Ya Janye Kalaman Sa Ko Kuma Su Gurfanar Dashi Kotun Musulunci
Ƙungiyar Matan Kannywood Sun Baiwa Sarkin Waƙa Kwana 3 Ya Janye Kalaman Sa Ko Kuma Su Gurfanar Dashi Kotun Musulunci |
Biyo bayan da furucin da Naziru Sarkin Waƙa yai akan cewa wasu daga cikin Jaruman finafinan Hausa na Kannywood mata kafin a saka su a cikin film sai anyi lalata dasu sannan ake saka su. Wannan Kalaman dai sun jawo cece-kuce a masana'antar inda jarumai mata suka magantu.
Sai dai ƙungiyar matan Kannywood ɗin sun kasa yin haƙuri ga wannan kalaman na Sarkin Waƙa inda suka saki wata wasiƙa tare da yin kira gareshi akan ya fito ya janye kalaman sa da yai akan su ko kuma su gurfanar dashi a gaban kotun musulunci domin yi musu Shari'a.
Ga dai abinda saƙon wasiƙar kamar haka;
Assalamu Alaikum!
"Ƙungiyar mata ta Kannyowood da ake kira da Women Association Nigerian (k-wan) ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar, Ni shugabar ƙungiyar a madadin ƴan ƙungiya.
Duba da abinda ya faru wanda Naziru M Ahmad ya yi wasu Kalamai na cin zarafi ga mata masu sana'ar film, muna kira a gare shi da ya janye kalaman sa cikin kwana 3 daga yau, idan kuwa bai yi hakan ba za mu kaishi kotun Muslunci bisa tuhumar da yi mana ƙazafi."
Nagode
Hauwa A Bello
Shugaba
Wannan itace wasiƙar da ƙungiyar matan Kannywood suka rubutawa Sarkin Waƙa. Abin jira dai agani shine ko Naziru zai fito ya janye kalaman nasa ko kuma ba zai janye ba, lokaci ne dai kaɗai zai tabbatar da hakan.
Tun a makon jiya ne dai bayan wata hira da aka yi da ɗaya daga cikin tsofaffi a masana'antar Kannywood Ladin Cima wanda ta bayyana cewa ba'a taɓa biyan ta kuɗi sama da dubu 5 ba a duk lokacin da ta fito a cikin Film ba. Wanda hakan ya jawo cece-kuce inda har wasu daga cikin jarumai suka ƙaryata kalaman tsohuwar.
Dalilin hakan ne yasa Sarkin waƙa ya fito ya mayar musu da martani wanda a cikin Kalaman sa ya bayyana cewa duk abinda tsohuwar ta faɗa gaskiya ne, domin duk tsofaffi ba'a biyasu wasu kuɗi masu kauri. Sannan kuma yace wasu ƴan matan ma ba'a saka su a cikin Film sai anyi lalata da su.
Leave Comments
Post a Comment