Tashin Gobara Yayi Sanadin Mutuwar Mutum 1 Tare Da Jikkata 17 A Maiduguri - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Tashin Gobara Yayi Sanadin Mutuwar Mutum 1 Tare Da Jikkata 17 A Maiduguri

Tashin Gobara Yayi Sanadin Mutuwar Mutum 1 Tare Da Jikkata 17 A Maiduguri
Tashin Gobara Yayi Sanadin Mutuwar Mutum 1 Tare Da Jikkata 17 A Maiduguri


Wata gobara da ta tashi a ranar juma'a a sansanin ƴan gudun hijira na Kalari dake a birnin Maiduguri na Jihar Borno wanda ya jawo mutuwar mutum 1 tare da jikkata wasu. Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar NEMA ita ce ta tabbatar da faruwar gobarar.


Abduƙadir Ibrahim shine kakakin NEMA a yankin arewa maso gabas, a wata tattaunawa da aka yi dashi ya yi bayanin cewa mutane 17 ne suka jikkata a cikin wanda gobarar ta rutsa dasu yayin da wani mutum ɗaya ya mutu.


Ya ƙara da cewa a ƙalla rumfuna 100 ne suka lalace wanda ya sa mutanen da ke zaune a cikin gidajen suka bar wajen bayan tashin gobarar. Gobarar ta tashi ne daga ɗaya daga cikin rumfuna dake wajen misalin ƙarfe na rana lokacin da suke yin girki a cikin wajen, a cewar Abdulkadir.


Ya bayyana cewa an yi nasarar kashe wutar bayan da jami'an kashe gobara na jihar suka kawo ɗauki inda suka kashe gobarar. Sai dai tuni hukumar NEMA, Red Cross da sauran masu ruwa da tsaki suka fara kai agaji ga waɗanda lamarin ya shafa domin ceto rayukansu.


An bayyana cewa sansanin na Kalari na ɗauke da gidaje a ƙalla 10,000 da kuma mutane fiye da 5,000 da suke yin rayuwa a ciki. Abdulƙadir yace jami'an NEMA da ba hukumar bayar da agajin gaggawa ta jiha SEMA su ne suka je suna auna irin illar da gobarar ta yi a cikin sansanin na ƴan gudun hijira.


Ana yawan samun tashin gobara a sansanin ƴan gudun hijira, ko a shekaru biyu da suka gabata an taɓa samu irin hakan a jihar Adamawa inda hakan yai sanadin mutuwar mutane sama da 10 wanda kuma ƙananan yara sunfi yawa.


A ƙarshe dai Hukumomin sun ƙara jan hankalin mazauna sansanin da du ringa kiyayewa kuma su kula a duk lokutan da suke yin girki ko kuma yin amfani da abinda ya shafi wuta domin kiyaye ƙara faruwar hakan anan gaba.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel