Ta Ya Ake Gane Discharge (Fitar Ruwa Daga Zakari ) Mai Matsala Ga Maza — Android Pols

Ta Ya Ake Gane Discharge (Fitar Ruwa Daga Zakari ) Mai Matsala Ga Maza
 Ta Ya Ake Gane Discharge (Fitar Ruwa Daga Zakari ) Mai Matsala Ga Maza  


Fitar Discharge daga al'aurar namiji na iya zama na al'ada ko kuma yana nuni da matsala, gwargwadon yadda yake da kuma wasu alamomi da suka biyo baya. Ga yadda za'a iya gane lokacin da wannan discharge na al'aurar namiji zai zama matsala:


Alamomin Da Ke Nuni Da Matsala 


1. WARI SOSAI: idan discharge yana ɗauke da warin da ba na al'ada ba, yana iya nuni da infection (misali, gonorrhea ko chlamydia). Warin mai ƙarfi ko wanda ba a saba da shi ba yana nuni da matsala.


2. JIN ZAFI YAYIN FITAR DISCHARGE: Idan lokacin da farin ruwan zai fita yana tashi tare da zafi ko jin zafi yayin fitsari, wannan na iya zama alama ta matsalar lafiya kamar urinary tract infection (UTI) ko kuma wasu cututtuka na dalilin saduwa daga Mai cutar (sexually transmitted infections ) (STIs).


3. KUMBURI KO JA: Idan gaban namiji ko gefe na al'aura yana kumbura ko ja, wannan na iya nuna infection ko matsalar jiki.


4. YAWAN FITAR DISCHARGE: Idan discharge yana fitowa fiye da yadda aka saba ko yana dauke da ƙyallen jini, wannan na iya zama alama ta prostatitis ko wasu matsalolin garkuwar jiki.


5. JIN ZAFI A CIKIN CIKI KO MARA: Idan matsalar ta haɗa da zafi a cikin ciki ko yankin pelvik (cikin ƙasan ciki), wannan na iya zama alama ta infection ko inflammation.


6. JIN ZAFI A LOKACIN MU'AMALAR AURE: Idan akwai jin zafi ko rashin jin daɗi yayin saduwa ko yayin fitsari, yana nuni da matsala.


7. DISCHARGE YAYI JA KO RUWAN ZINARE: Launin ruwan zinare ko ja yana nuni da infection ko bacterial urethritis.


SHAWARA

Idan akwai wasu daga cikin alamomin da aka lissafa a sama, ya kamata a tuntuɓi likita don gwaje-gwaje da duba lafiyar al'aurar. Likita zai iya duba samfurin discharge don gano ko akwai kwayoyin cuta, wanda zai taimaka wajen samar da magani.


Gudanar da Gwaje-Gwaje: Likita zai iya gudanar da gwaje-gwaje na jini ko fitsari don tabbatar da ko akwai infection ko wata matsala mai alaka da STIs ko UTI.


Allah yasa mu dace


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post