Sojin Najeriya Sun Kai Hare-Hare Ga Mayaƙan ISWAP Sun Hallaka Manyan kwamandojin Su
Sojin Najeriya Sun Kai Hare-Hare Ga Mayaƙan ISWAP Sun Hallaka Manyan kwamandojin Su |
Jiragen Sojojin Najeriya sun kai wasu hare-hare na luguden wuta ga maɓoƴar mayaƙan ƴan ISWAP wacce suke cin karen su babu babbaka a ƙauyukan jihar Borno. A yayin kai harin ne dai aka kashe aka kashe Amir Ɗanfulani da wasu manyan kwamandojin ƙungiyar.
Wata majiya ta tabbatar da cewa sojojin sun kai hari ne inda suka samu nasarar kashe da yawa daga cikin mayaƙan na ISWAP, sun kai harin ne a Jiragen sama masu ƙirar Super Tucano wanda nallakin rundunar sojin sama ne. A harin dai baya ga Amir Ɗanfulani akwai wasu da dama da aka kashe.
Harin ya yi sanadin mutuwar wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ta ISWAP wanda har da Malam Ari wanda shine ke lura da yankin na Kirtab Wulgo. Wani jami'in soja ya bayyana cewa hare-haren da aka ƙaddamar sun samu wani rahoton sirri inda mayaƙan suka ɓoye, wanda kuma muka yi amfani da wannan damar muka afka musu.
Mayaƙan na ISWAP kusan su 40 ne suke a ɓoye a yankin kirta Wulgo, inda suka kafa tutar su wanda yake nuna cewa sune ke da mallakar garin. Suna amfani ne da wajen suna domin harba makami mai linzami kan sansanin sojojin Najeriya dake a Malam Fatori. Wanda hakan yasan rundunar sojin sama ta operation Haɗin kai ta tura wasu jirage ta wajen.
Wanda kuma suka yi nasarar tarwatsa maharan tare da lalata wajen da suke ɓuya. Harin dai yai sanadin mutuwar manyan kwamandojin ƙungiyar su 4 tare da wasu da dama daga cikin yaran su. Sai dai kuma wasu da dama daga cikin su sun yi nasarar tserewa daga wajen.
A baya-baya nan dai rundunar sojin Najeriya suna ƙoƙarin sosai wajen daƙile ayyukan mayaƙan ISWAP da suka addabi yankin arewa maso gabas. A duk lokacin da rundunar ta kai hari a jiragen ta na yaji ta kan yi nasarar kashe da dama daga cikin maharan na ISWAP.
Hakan yasa jama'a a Jihar Borno da ma faɗin ƙasa ke yabawa jami'an sojin kan irin ƙoƙarin da suke yi wajen Murƙushe mayaƙan a duk inda suke. Haka kuma ana yabawa gwamnan jihar Babagana Zulum kan jajircewar sa wajen ganin jihar ta samu. Zaman lafiya kamar yadda take a shekarun baya.
Leave Comments
Post a Comment