Sojin Najeriya Sun Hallaka Kwandojin ISWAP Su 50 A Wani Harin Ramuwar Gayya Da Sukai Kaiwa Ƙungiyar - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Sojin Najeriya Sun Hallaka Kwandojin ISWAP Su 50 A Wani Harin Ramuwar Gayya Da Sukai Kaiwa Ƙungiyar

Sojin Najeriya Sun Hallaka Kwandojin ISWAP Su 50 A Wani Harin Ramuwar Gayya Da Sukai Kaiwa Ƙungiyar
Sojin Najeriya Sun Hallaka Kwandojin ISWAP Su 50 A Wani Harin Ramuwar Gayya Da Sukai Kaiwa Ƙungiyar



Daga Jihar Borno wani rahoto daga Hedkwatar tsaron  Najeriya tace sojojin ƙasa ta Najeriya sun yi wa mayaƙan Boko Haram luguden wuta a ƙauyen Leho na arewacin jihar Borno. 


Birgediya Janar Onyema Nwachukwu wanda shine kakakin rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya yace sojojin Operation Haɗin Kai sun kashe wasu daga cikin manyan kwamandojin mayaƙan ISWAP a ƙalla su 50 tare da lalata makaman su a harin ramuwar gayya da suka kai wa ƴan ƙungiyar a ƙaramar hukumar Askira Uba dake a yankin jihar Borno.


A yayin kai harin ne tawagar sojin suka lalata motocin mayaƙan irin na yaƙi masu ɗauke da sulke sama da 10 cikin motocin akwai tarin bindigogi masu tarin yawa da aka lalata. Ance bindigogin masu haɗari ne wanda su kan su jami'an sojin ba sa amfani da irin su, amma dai duk sojojin sun lalata makaman na ƴan ISWAP ɗin.


Farmakin da sojojin su kai kaiwa ƴan bindigar na da nasaba da ramurwar gayya biyo bayan wani hari na ba zata da ƴan bindigar suka yi a kwanakin baya wanda yai sanadin mutuwar babban kwamandan runduna ta 28, Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da sauran wasu jami'an soji su 3 da suke aiki a ƙarƙashin sa a yankin a Askira Uba.


Tun a ranar Asabar ne dai tawagar ƴan bindgar suka kai wa jamian soji wani hari a sansanin runduna ta 28 ta sojin ƙasa hari a garin na Askira Uba, inda biyo bayan muayasar wutar ne Janar Dzarma da sauran yaran sa suka rasa rayukansu, wanda ake ganin cewa mutuwar Dzarma babban rashi ne ga rundunar sojin Najeriya duba da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen murƙushe mayaƙan ISWAP ɗin.


Biyo bayan harin da ƴan bindigar suka yi yasa suma rundunar soji suka mayar da martani inda suka bi mayaƙan har maɓoƴar su inda suka yi musu luguden wuta ta sama da ƙasa wanda hakan ya jawo mutuwar manyan kwamandojin ƙungiyar a ƙalla su 59 tare da jikkata wasu da dama da ba'a bayyana adadin su ba, inda wasu kuma suka samu tserewa.


Mayaƙan na ISWAP sun kwashi kashin su a hannun ne tun bayan da rundunar soji ta 115 suka yi musu shigar sauri da sanyin safiya da ruwan wuta ta sama da ƙasa wanda hakan ya firgita mayaƙan inda suka ringa gudun neman tsira da rayukan su. Wasu da dama sun yi nasarar guduwa yayin da kuma wasu suka mutu wasu kuwa suka ji mummunan raunuka.


Nwachukwu yace sun tsinci gawarwarkin wasu manyan mayaƙan ƙungiyar tare da kame wasu daga cikin su da suka ji manyan raunuka babu damar guduwa. A rahoton da rundunar ta soji ta fitar a ranar Litinin.


Mayaƙan dai sun daɗe suna barazana ga rayukan al'umma a cikin gari da Ƙauyukan jihar ta ta Borno, tare da mallake wasu yankuna da dama a jihar da kuma sace dukiyoyi da kayan amfanin gonar al'umma. Sai dai rundunar sojin ta na iya ƙoƙarin ta na ganin sun daƙile irin wannan hare-haren da mayaƙan suke kaiwa.


Jihar ta Borno dai ta shafe kusan shekaru 12 kenan tana fama da matsalolin ƙungiyar Boko Haram tare da kashe mutane da jami'an tsaro har da lalata dukiyoyin gwamnati da na jama'a. Hakan dai ya biyo bayan Shugaban su na farko da yace yin Boko haramunne wanda jami'an ƴana Sanda suka hallaka shi.


Tun bayan hakan ne dai ake ta samun ƙaruwar mayaƙan na Boko Haram wanda har daga baya aka samu shigowar ISWAP su ma suna ta kai hare-hare tare kashe al'umma. Sai dai gwamnati tace tana yin ƙoƙarin ta wajen shawo kan matsalar.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel