Sirrin Haɗin Tumatur Da Kurkur Domin Gyaran Jiki Da Fata — Android Pols

Sirrin Haɗin Tumatur Da Kurkur Domin Gyaran Jiki Da Fata
Sirrin Haɗin Tumatur Da Kurkur Domin Gyaran Jiki Da Fata


Sirrin dake cikin Tumatur, Kurkur da Sukari da lemon tsami, wannan sirrin yana da matuƙar tasiri ƙwarai dagaske wanda bincike ya gano cewa suna da matuƙar tasiri ga fatar Ɗan Adam. A maimakon abubuwan da kuke siya na man shafawa ko kuma abubuwan da ke canja fata, wannan haɗin zai yimiki duk abinda kikeso a fatar ki. Idan ke baƙa ce ke zai ƙara miki haske da yimiki maganin dukkan wasu ƙuraje a fuskar ki da jikin ki tare kuma da ƙarawa fatar lafiya, wannan shine sirrin.


Ƴan uwa idan kuna so kuyi amfani da maganin da zai gyara muku fatar jikin ku ko canja launin fata ba tare da fargabar abinda zai biyo baya ba to kuyi ƙoƙarin yin amfani da waɗannan abubuwan da za mu sanar daku a wannan rubutun. Kaso 80 na magunguna da suke gyara fata su canja launin ta suna haifar da matsala ga fata wanda a lokacin da kake amfani bazaka san hakan ba sai daga baya. Amma shi wannan da za mu baku aiki 2 zai yi muku a fatar ku bayan gyara ta zai kuma inganta lafiyar fatar.


Sirrin Haɗin Tumatur Da Kurkur Domin Gyaran Jiki Da Fata


Domin yin wannan haɗin ku nemi wannan abubuwan kamar haka;


(1) Kurkur, ku nemi busasshe sannan sai ku daka shi ku tankaɗe yai gari.

(2) Tumatur (tomato) ku nemi mai kyau jajur ki raba shi biyu.


Zaki ringa dangwalar garin kurkur ɗin da wannan tumatur ɗin da kika yanka kinan gogawa a fuskar ki da jikin ki. Duk inda kikeso ki goga a jikin ki zaki iya yi. Idan kin goga sai kibarshi kamar tsawon minti 20 sai ki samu ruwa ki wanke wanke. Haka zaki ringa yi kullum, ba zaki sati biyu ba sai kinga yadda fatar jikin ki zata canja.


Idan inda kuke babu waɗannan abubuwan da muka ambata, to ga wani haɗin shima da zaku yi amfani dashi da zai gyara muku jikin ku. Zaku nemi waɗannan abubuwan kamar haka;


(1) sukari, kamar cokali ɗaya da rabi wato 1/2

(2) Sai ku samu lemon tsami ƙarami guda 1 a yanka shi 


Wannan sukarin za ku ɗiba ku zuba a cikin wani mazubi mai kyau sai ku matse wannan ruwan lemon tsamin a ciki sai ku juya shi sosai su haɗe. Idan akwai garin kurkur zaku iya zuba kamar cokali 1 ku haɗa ku juya idan kuma babu sai kuyi amfani dashi a haka. Shima zaku ringa shafawa a duk inda kuke so a jikin ku, duk inda wasu ƙuraje ko ƙyasbi dake damun ku a fata za kuyi maganin sa. Wannan haɗin ana iya shafa shi a ko ina a jiki banda dubura da gaban mace ko gaban namiji.


Idan an goga a barshi na tsawon minti 30 sannan sai a wanke da ruwan ɗumi. Idan kuma duka jikin ne aka shafa to ruwan ɗumin dai za'a samu a shiga banɗaki a wanke jikin dashi. Kuyi kamar sati 2 kuna yin amfani da wannan sinadaran za ku ga yadda fatar ku za ta canja ta yi kyau.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post