Sirrin Haɗin Ruwan Tafarnuwa Da Ɗanyar Citta — Android Pols

Sirrin Haɗin Ruwan Tafarnuwa Da Ɗanyar Citta
Sirrin Haɗin Ruwan Tafarnuwa Da Ɗanyar Citta


Yau za mu yi bayani akan gyaran jiki, kamar yadda kuka sani kwanakin baya munyi jawabi akan yadda za kuyi amfani da tafarnuwa wajen gyara jiki, sai dai wasu daga cikin masu bibiyar mu suna ta turo da saƙo akan basu fahimta ba to shine yau muka shirya yi muku bayani sosai akan yadda za kuyi amfani dasu. Wannan sirrin ni kaina kullum ina yin amfani dashi safe da yamma.


Wallahi wannan sirrin idan kina amfani dashi babu ruwanki da wani man shafawa na ƙara hasken jiki da sa fata ta yi kyau. Fatar ki zaki ga tana laushi, kuma za kiga fuskar ki tana sheƙi, idanu za suyi haske haƙora su fari suyi haske. Gashin jikin ku za kuga yadda zai yi laushi yai baƙi. 


Sannan kuma duk wani tsohon sanyi da ke jikin ku wanda yake yin tasiri a jikin fata da wanda yake tasiri a baki ko amosanin kan mutum kai duk wani abu da ya shafi fata indai za ku mayar da wannan haɗin ruwan shan ku a kullum to za ku yi matuƙar mamakin yadda jikin ku zai canja.


Sirrin Haɗin Ruwan Tafarnuwa Da Ɗanyar Citta


Abinda nace ku nema shine Tafarnuwa da kuma Citta ɗanya. Za ku sami tafarnuwa ƙwallo ɗaya, wato mai sili 5 ko 6 sai ku ɓare ta. Ku samu ruwan roba kamar swan ko faro sai ku zuba wannan tafarnuwar da kuka ɓare a cikin robar ruwan. Sai ku samu ɗanyar citta ku ɓare ɓawon ku yayyanka ta ku zuba a cikin ruwan robar wato ku haɗa da wannan tafarnuwar da kuka zuba a cikin ruwan robar ku rufe ku barshi yai kwana 1.


Ku sami kofi mai kyau kuna zuba ruwan kuna sha, ana so ku mayar dashi ruwan shan ku. Idan ruwan ya ƙare sai ku zubar da diddigar dake cikin robar ku ƙara zuba wata tafarnuwa da ɗanyar citta kamar yadda kuka yi na farko ku rufe ya kwana ku cigaba da sha. Wallahi duk wanda zai juri yin wannan haɗin kuma yana sha a kullum to duk wasu ƙuraje da gishirin hanci ko wani ƙaiƙayin jiki dake damun mutum, duk wani abu da ya danganci jikin fata to zai yi muku maganin sa.


Kamar yadda na faɗa muku ni wannan sirrin nawa ne domin ni kullum dashi nike yin amfani kullum sai nasha wannan haɗin kuma ina jin daɗin sa. Sauran jama'a da yawa suna amfani dashi kuma suna yi mana godiya. Don haka kuma kuyi ƙoƙari ku haɗa shi ku ringa yin amfani dashi, musamman mata ku zai fi muku amfani saboda su mata ana so ko yaushe su ringa yin gyaran jikin su. Domin idan kika riƙe wannan haɗin kina shan sa a kullum to babu ke babu siyan wasu kayan mai na gyran fata. Ina fatan ba za kuyi wasa da wannan sirrin na haɗin ruwan tafarnuwa da ɗanyar citta ba.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post