Sirrin Ɗanyen Ƙwai Da Zuma Domin Matan Da Suke Da Raunin Sha'awa |
Mata ku tsare gidajen ku, ku tsare mazajen ku, ku hanasu fita suna kallace-kallacen wasu matan, ya kalli waccen yaje wajen waccen, to ki tsare kayan ki fa kuma babu yadda za'ai ki tsare kayan ki sai kin kasance babu kamarki a wajen sa kuma babu yadda za'ai ki zama hakan dole sai kina gyara jikin ki. Yawancin matan da mazan su ke fita waje suna kula wasu matan sunfi matan da mazan nasu suke kulawa a wajen. Amma saboda rashin kula da rashin gyara jiki wanda hakan ke jawo mazan su fara sha'awar wasu matan na waje.
Abubuwan da kike dashi da ƙimarki da kyan jikin ki da kyan dirin ki da darajar ki yafi na waccen matar ta waje da take birge mijin naki. Wataƙila dai ta fiki yin gyara da iya kwalliya da kuma tarairaya. To amma fa anan muna jan hankalin maza masu ɗabi'ar kula wasu matan na waje musamman waɗanda ba da niyyar yin aure ba da su sani cewa duk wanda yake kula matar wani shima za'a yiwa matarsa, kuma duk wanda yake yiwa ƴaƴan wasu wani abu da bai dace ba to yasani shima za'a yiwa nasa ƴaƴan.
Don haka maza ku tsare mutuncin ku da imanin ku, ku auri matan da kuka tabbatar da tarbiyyar su da ilimin su, amanar su da kuma tsaftar su, waɗanda idan sun yi kwalliya sunyi ado zasu burgeku. Ku siya mata dukkan kayan da kuke ganin idan matan waje sun sa suke birge ku. Idan zaka ringa siya mata irin waɗannan kayan kana kawo mata tana sawa zakaga tafi ta wajen komai da komai. Indai zaka kayutatawa matar ka ta gida to babu wata mace a waje da za taja hankalin ka har kaji tafi matar ka.
Ka siya mata kayan gyara jiki irin su maya-mayai da turaruka wanda idan tasa za ta birgeka. Ko kuma ka bata kuɗin ta siya da kanta domin ita za ta fika sanin waɗanda idan ta yi amfani dasu zasu birgeka. Ka siya mata dukkan wani abu wanda idan ta saka ko ta shafa zai sa kaji daɗi. Amma idan ka siya mata irin wannan kayan idan kuna da yara sai ku bari sai sun tafi makaranta ko kuma idan sunyi bacci. Amma idan kana da wajenka shikenan sai ta yima kwalliya ta sa duk irin kayan da idan kagani zaka firgita don sha'awa.
Ga wani haɗin ɗanyan ƙwai da zaki amfani dashi, wannan haɗin na musamman ne domin yana ƙarawa mace kuzari ba tare da ta gaji ba a yayin da mijinta ke saduwa da ita ba sai sai shi ya gaji idan baya shan maganin sanyi. Amma ke ba za ki gaji ba idan kina yin wannan. Abubuwa 2 kawai zaki nema, ki samu ganyen shayi ko wane iri ne ki zuba ruwa kamar rabin kofi ki saka wannan ganyen shayin a ciki, sannan ki samu ɗanyen ƙwai ki fasa ƙwai ki zuba a cikin wannan kofin na ganyen shayi.
Ki samu zuma kadan ki zuba sannan zaki iya ƙarawa da madara ki juya sai ki shanye. Ranar idan mijinki zai sadu dake zakiji wani ƙarfin sha'awa a tattare dake, kuma ko zuwa nawa zai yi a wannan lokacin ba zaki gaji ba. Amma wannan haɗin ga matan da basa iya jure jima'i ne idan mazan su suna saduwa dasu. Domin wasu matan basa iya jurewa ayi jima'i dasu na tsawon minti 30. To idan kinsan kina da wannan matsalar ki ringa haɗa wannan kina sha.