Shawarwari 10 Ga Yaro Game Da Mai Gidansa - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Shawarwari 10 Ga Yaro Game Da Mai Gidansa

Shawarwari 10 Ga Yaro Game Da Mai Gidansa
Shawarwari 10 Ga Yaro Game Da Mai Gidansa 



1- Dole ka riƙa girmama mai gidanka, da mutunta shi da karrama shi, da ba shi matsayinsa na mai gida, koda ka girme shi a shekaru. Matuƙar kana son ci gaba, to dole ka girmama wanda yake gaba da kai. Bahaushe na cewa "yaro ba ya raina manya ya yi ƙarko" wannan gaskiya ne, kuma wannan magana tana shiga kusan kowanne babi na mu'amala; kasuwanci ko karatu ko addini da sauran sabgogi na zamantakewa.


2- Kada ka yi wani abu da zai riƙa jefa zargi cikin zuciyar mai gidanka game da kai, domin daga lokacin da mai gidanka ya rasa natsuwa da kai, ya fara tuhuma da zarginka jin daɗin zamanka da shi ya zo ƙarshe.


3- Kada ka bayyana wa mai gidanka kaifin basirarsa da ƙololuwar kwarewarka da iya magana da sauransu, kada ka riƙa fin mai gidanka iya wanka da kwalliya da kashe kuɗi da makamantansu, domin zai fara jin kamar ka ɗauki hanyar yi masa juyin mulki. Shi ya sa mai littafin 48 Laws of Power, ya buɗe littafin da "Never outshine your master" don haka koda ka fi shi baiwa, to kada ka bayyana masa, ka sanya a tunaninsa ya riƙa jin sama yake da kai.


4- Kada ka taɓa zama ƙarƙashin mai gidanka ba tare da kana da shirin tsayuwa da ƙafarka ba, duk irin gata da kyautatawa da yake maka, ya zama kai ma kana da hadafin zama mai gidan kanka.


5- Galibin iyayen gida ba su son yaronsu na amana ya ɓalle daga gare su, dole ka san wannan sosai. Musamman yaro mai amana, wanda ya san sirrin kasuwancin mai gidansa. Shi ya sa wasu masu gidan da gangan suke daƙile ci gaban yaransu domin kada su girma su yi fukafukai, su fire su bar su, wasu mara sa imanin har da asiri suke turke yaransu.


6- Kada ka sake ka bari mai gidanka ya san shirinka na tsayuwa da ƙafarka, domin daga lokacin da ya sani, wani zai fara canja maka, ko kuma ƙoƙarin daƙile ka.


7- Kada ka ɓalle daga mai gidanka sai ka tabbata ka kai matsayin da za ka iya tsayuwa da ƙafarka, kada ka yi gaggawa, kuma ka yi haƙuri, ka bi komai a sannu, domin rashin iya tsayuwa da ƙafa bayan ɓallewar zai sanya ka yi biyu babu.


8- Daga lokacin da ka bayyana wa mai gidanka shirin ɓallewa to ka sani daga lokacin ya cire ka a fakaice, koda ba ka ɓalle ba, zai sauya maka, kuma ba zai ƙara bari ka san sirrin abubuwan da ake yi ba.


9- Idan ka riga ka ɓalle, to ba za ka sake dawowa ba, koda ka yi rashin nasara (Allah Ya tsare) kada ka dawo, ka nemi wani wajen kawai, ya zama tsakaninku mutunci ne da girmamawa kawai, domin idan ka dawo koda ya karɓe ka ba zai saki jiki da kai ba.


10- Idan za ka rabu da mai gidanka, duk da cewa ba zai so ku rabu ba, ka yi iya ƙoƙarinka ka ga kun rabu lafiya, ka yi haƙuri da duk abubuwan da za a riƙa faɗa, don ka rabu da mai gidanka da nufin tsayawa da ƙafarka ba ka yi wa kowa laifi ba, ba ka yi butulci ba. Kowa yana da haƙƙin ya cim ma burinsa na rayuwa. Don a yi abin da kake ganin maslaha ne ga rayuwarka kuma ba ka taɓa haƙƙin kowa ba, kada ka ji a ranka ka yi laifin komai.

Allah Ya ba mu sa'a.


✍️ Isa Sadi 


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel