Shawarari Domin Kiyaye Mutuwa Bakatatan Yayin Atisaye Ko Motsa Jiki — Android Pols

Shawarari Domin Kiyaye Mutuwa Bakatatan Yayin Atisaye Ko Motsa Jiki — Android Pols
Shawarari Domin Kiyaye Mutuwa Bakatatan Yayin Atisaye Ko Motsa Jiki  


Idan ka san ba ka motsa jiki akai-akai sai wani dalili da ke buƙatar motsa jiki mai tsanani ya zo maka, misali, wasan ƙwallon ƙafa, gasar tsere, atisayen shiga rundunonin tsaro da dai sauransu, to akwai buƙatar yin shiri gabanin fara wannan motsa jiki domin shirya zuciya don fuskantar motsa jiki mai tsanani.


Saboda haka, akwai buƙatar aƙalla kwanaki uku ana shirya zuciya domin aikinta ya bunƙasa kafin fara motsa jiki mai tsanani, misali, ya kamata mutum ya fara da matsakaitan motsa jiki kamar tafiya, sauri, sassarfa sannan sai gudu aƙalla na minti 30 — 40 kullum tsawon kwanaki uku.


Hakan zai taimaka wajen shirya zuciya domin fuskantar babban ƙalubalen motsa jiki mai tsanani.


Bugu da ƙari, idan ka san likita ya tabbatar maka da wata lalura kamar hawan jini, ciwon siga ko ciwon zuciya kuma ka san ba ka motsa jiki akai-akai tabbas akwai buƙatar shawarar likita kafin fara motsa jiki ko atisaye mai tsanani.


Rashin shirya zuciya gabanin fara motsa jiki ko atisaye mai tsanani na iya janyo bugun zuciya wace ke sanadiyyar mutuwar mutum nan-take.


© Physiotherapy Hausa


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post