ShanyewarƁarinJiki — Me ke faruwa a ƙwaƙwalwar?
ShanyewarƁarinJiki — Me ke faruwa a ƙwaƙwalwar? |
Shanyewar ɓarin jiki na iya faruwa ga kowa, a kowane lokaci kuma a ko ina. A yau, shanyewar ɓarin jiki shi ne jagaba wajen nakasa mutane a faɗin duniya kuma na biyu a jerin cutukan da suka fi hallaka mutane. Sai dai, duk da hakan, hukumomin kiwon lafiya sun ce, za a iya kiyaye har kaso casa'in cikin ɗari (90%) na shanyewar ɓarin jiki matuƙar mutane na bin hanyoyi da matakan kiwon lafiya da suka haɗa da: kiyaye hawan jini, cin lafiyayyen abinci, guje wa taba sigari, gujewa wa barasa / giya, guje wa ƙiba / teɓa da kuma motsa jiki / atisaye akai-akai.
Shanyewar ɓarin jiki na faruwa ne sakamakon lahani ga ƙwaƙwalwa.
A shanyewar ɓarin jiki, ƙwaƙwalwa na samun lahani ne ta hanyoyi biyu kamar haka:
1. Toshewar jijiyar jini: Toshewar jijiyar jini na faruwa ne yayin da jini ya daskare a cikin manya ko ƙananun jijiyoyin jini a sassan jiki, sannan ƙwayar daskararren jinin ta ɓalle zuwa siraran jijiyoyin jini a can ƙwaƙwalwa. Har wa yau, ɓirɓishin kitse da ke kwance a jijiyoyin jini na iya ɓallewa sannan ya tafi zuwa jijiyar jini a ƙwaƙwalwa har ya toshe ta.
2. Fashewar jijiyar jini: Yau da gobe, siraran jijiyoyin jini a ƙwaƙwalwa na ƙara yin rauni, saboda haka, haɗarin fashewarsu ke ƙaruwa da miƙawar shekaru. Kuma haɗarin fashewar na ƙaruwa ne da ƙarin matsaloli kamar hawan jini da shan taba sigari.
A kowane irin shanyewar ɓarin jiki da ya afku, katsewar jini zuwa wani sashin ƙwaƙwalwa ne ke faruwa. Kuma katsewar jini na nufin katsewar iskar oksijin da gulukos zuwa wannan sashi na ƙwaƙwalwa. Bugu da ƙari, toshewar jijiyar jini a ƙwaƙwalwa na tsawon minti ɗaya tak na iya hallaka ƙwayoyin halittar ƙwalƙwawa har miliyan biyu.
Kuma katsewar jini ga wani sashin ƙwaƙwalwa na nufin katsewa ko raunin aiki a sassan jiki wanda ƙwaƙwalwar ke sarrafa su, kamar hannu, ƙafa ko sassan furuci.
Duba yadda za ka gane alamun shanyewar ɓarin jiki da abin da ya kamata ka yi.
Leave Comments
Post a Comment