Labaran Duniya
Shahararren Mai Kuɗi A Nahiyar Afirka Aliko Ɗangote Yayi Babban Rashin Ƙanin Sa Sani Ɗangote Bayan Gajeriyar Rashin Lafiya A Amurka
Monday, January 20, 2025
0
Shahararren Mai Kuɗi A Nahiyar Afirka Aliko Ɗangote Yayi Babban Rashin Ƙanin Sa Sani Ɗangote Bayan Gajeriyar Rashin Lafiya A Amurka |
Ƙani ga babban mutum kuma shahararren ɗan kasuwa a Nahiyar Afirka Alhaji Aliko Ɗangote ya rasu bayan shafe tsawon lokaci yana fama da jinya.
A safiyar ranar Litinin ne Allah yaiwa Alhaji Sani Ɗangote rasuwa wanda ƙarni ne ga fitaccen mai kuɗi a Najeriya da kuma nahiyar Afirka Alhaji Aliko Ɗangote. Marigayin wanda shine mamallakin kayan noma da dangogin su na 'DANSA' wanda yake mallakin Aliko Ɗangote.
Wata majiya ta tabbatar da cewa Alhaji Sani ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti dake a kasar Amurka bayan fama da rashin lafiya. Wanda ya shafe kwanaki a can yana jinya. Kafin rasuwar sa Alhaji Sani ya shafe shekaru 30 yana gudanar da harkokin kasuwancin sa musamman a ɓangaren masana'antun kayan noma da harkokin mai.
Baya ga haka kuma Alhaji Sani ya riƙe manyan muƙamai a kamfanoni da dama ciki har da kamfanin saƙa da ake kira da textile da Kamfanin alawoyi na Nutra Sweet da kamfanin masaƙar Ɗangote Textile da kamfanin lemuka na Dansa da kuma Ɗangote farms da dai sauran manyan kanfanoni wanda nallakin Aliko Ɗangote ne.
Wata majiya ta ce Aliko Ɗangote ya nuna kaɗuwar sa sosai da mutuwar ƙanin nasa wanda aka ce suna kallon sa kwance a kan gado a lokacin da aka zare ransa. Muna kallo nida mahaifiyar mu a lokacin da ƙanin nawa ya rasu ba za mu iya yi masa komai ba na hanashi mutuwar ba har Allah ya ɗauki abin sa, a cewar Aliko Ɗangote.
Wannan ke nuna cewa duk gatan mutum kuma duk dukiyar da yake da ita indai mutuwa tazo to babu makawa sai an tafi, babu jira ko da na minti ɗaya ne. Shi dai Alhaji sani rayuwar sa ta zo ƙarshe kuma gashi ya bar duniya bayan da ya shafe kwanaki yana jinya.
An bayyana Alhaji Sani a matsayin babban na hannun daman Aliko Ɗangote wajen tafiyar da harkokin sa na ciki da wajen Najeriya. Ance kuma sun daɗe suna gudanar da ayyukan kasuwanci tare ba tare da matsala ba shiyasa ake ganin cewa mutuwar tasa babban rashi ne ga Aliko wanda da wuya a maye gurbin sa.
Mutane da dama sun bayyana rasuwar Sani Ɗangote a matsayin babban rashi wanda ya saba taimakon al'umma da mabuƙata, ance mutum ne mai alheri da taimakon al'umma. Domin duk wanda ya san shi zakaji yana faɗan irin alherin sa da yake yiwa jama'a na gida da kuma waje.
Aliko Ɗangote ya bayyana rasuwar ƙanin sa a matsayin wacce ta girgiza shi kuma yace ba'a taɓa mutuwar da ta dimauta shi ba kamar ta
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment