Sanyi Kowane Irine Daga Jikin Ku — Android Pols

Yadda Zaku Kawar Da Sanyi Kowane Irine Daga Jikin Ku
Yadda Zaku Kawar Da Sanyi Kowane Irine Daga Jikin Ku


Barknmu da saduwa daku a wannan filin na magunguna. Indai matsala ce akan sanyi, ciwon mara, riƙewar ƙafa, zafin jiki, ciwon ido, ƙaiƙayin ido, ƙaiƙayin jiki da sauran su. Ciwon sanyi dai ciwo ne da yake damun kowa maza da mata domin da wuya ka samu cikin mutum 100 baka samu 90 suna da cutar sanyi ba.


Kamar yadda na faɗa shi wannan maganin sanyi ne da kowa zai iya yin amfani dashi maza da mata manya da yara. Sai dai kuma shi wannan haɗin ana so idan ma'aurata za su yi amfani dashi su yi su duka ma'ana idan kana da mata 1 ko mata 4 to ya kamata kusha shi duk a lokaci guda hakan shine zai yi muku maganin sanyin gabaki ɗaya.


Amma idan kai maigida kasha kuma matarka ko kuma matanka suna dashi to babu wani aiki da zai muku, koda yai muku aiki na kwanaki ne. Da fatan uwargia idan zaki wannan haɗin to ki tabbatar cewa kinyi shi ke da mijin ki domin idan baku sha tare ba to gaskiya ba zai miki wani magani ba domin idan shi yana da sanyin zai iya dawo miki dashi.


Maganin Sanyi Kowane Irine Daga Jikin Ku


Ga abubuwa guda 2 da za ku nema domin ku yi wannan haɗin maganin kamar haka;


(1) Madara ta ruwa, idan babu sai ku samu Nono mai kyau.

(2) Kaninfari, amma garin sa ake da buƙata idan babu garin sai ku daka shi ya zama gari.


Idan kun samu garin kaninfari ku ɗibi kamar rabin cokali ku zuba a cikin wannan madarar ko kuma nono ku juya sosai su haɗe sai ku shanye. Za ku yi haka har tsawon kwanaki 3. Ba za ku ƙara sha ba har sai bayan kwana 3. Haka za ku yi har tsawon kwanaki 9.  Indai matsala ce ta sanyi irin na mara to ku jarraba wannan haɗin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post