Maganin Basir Mai Tsiro |
Ga duk wanda yake fama da basir mai tsiro kowane iri ne. Akwai waɗanda basur yake yi musu tsiro yake fito musu a gefen dubura wasu kuwa kewaye duburar yake yi. Zaku gansu ƙanana sun fito. To duk wanda yake fama da wannan matsalar ga wani haɗin magani da za mu baku ku ringa sha.
Akwai Abubuwan da zaku haɗa kuyi amfani dasu domin kuyi maganin basir mai tsiro da yake fitowa. Abubuwan da zaku nema guda 3 ne kacal kamar haka.
(1) Man Tafarnuwa, ƙaramin coklai ko kuma babba duk yadda kuka sa yai daidai.
(2) Man Habbatus Sauda, shima kamar dai adadin na farko.
(3) Man Zaitun, shima yawan sa irin na farko da na biyu da muka ambata.
Sabon Haɗin Maganin Basir Mai Tsiro
Zaka iya haɗa su da yawa yadda zaka daɗe kana amfani da su idan basir ɗin yaima tsiro da yawa. Yadda zakai shine idan ka samu duk waɗannan abubuwan da muka ambata sai ka haɗe su waje guda, wato Man Zaitun, Man Tafarnuwa da Man Habbatus Sauda.
A duk lokacin da zaka kwanta za ka samu auduga sai ka dangwali wannan haɗin man sai ka yi ɗauke dashi, wato kayi matsi dashi. Audugar za ka saka a duburar ka. To insha Allah indai zaka juri yin hakan a kullum to duk wannan tsiro ɗin sai ya koma zaka neme shi ka rasa cikin ƙaramin lokaci.
Indai tsiro ne na basir to ku jarraba wannan haɗin. Sai dai anan muna kira ga jama'a da su daina yawan ci ko shan abubuwan da suke tayar da basir. Domin shi basir zafi ne wanda kuma duk maganin da za ka sha indai kana cin irin wannan abubuwan masu tayar da basir mai tsiro to za su yi ta dawo maka ne.