Sabon haɗin Girman Mazaunai Domin Mata — Android Pols

Sabon haɗin Girman Mazaunai Domin Mata
 haɗin Girman Mazaunai 


Bincike na musamman akan abinda ya shafi ƙarin girman mazaunai na mata wato (hips). Akwai bayani da yakamata mata ku sani akan mazaunai, domin halittar mata ta bambanta akwai matan da suke da kiɓa kuma suna da mazaunai daidai gwargwado. To irin wannan matan zai yi wuya kaga hips ɗin su ya fito fili, wasun su zakaga suna da mazaunai amma ba girman jiki wasu kuwa da girman jikin amma babu hips, wasu kuwa akwai nono amma babu mazaunai, wasu kuwa akwai hips amma babu nono. Wasu matan kuma zaka gansu da kiɓa amma ba hips kuma babu nono. 


Wasu matan kuma zaka gansu sirarara ne babu girman jiki amma kuma suna da hips manya. Wasu kuma zaka gansu dogaye ga girman nono amma kuma babu girman hips. To kusan dai kowace mace tana da irin nata halittar. To dole ne mata su san cewa ɗabi'ar ki daban take da ta waccen. Shiyasa koda magani na ƙara girman mazaunai a lallai idan kinyi amfani dashi kin samu waraka ba wata ma ta samu ba. Domin wannan haɗin da za mu baku wata idan ta yi amfani dashi sai da ta ƙara samun kiɓa a maimakon samun girman mazaunai.


Domin yawancin maganin da za'a baku ace zai ƙara muku girman jiki, girman nono, girman mazaunai ace iya shine kawai zai ƙara girma, abu ne mai wuya. Misali idan kinsha maganin da zai ƙara miki girman nono to ba iya girman nono zai ƙara miki ba har jikin ki zai iya ƙara girma. Shiyasa muke tunatar daku domin kada kisha magani kizo jikinki yai girma ki rasa ya akai hakan ya faru.


 Sabon haɗin Girman Mazaunai Domin Mata 


Ga yadda zaku haɗa wannan ga macen da take so ta ƙara girman hips. Wannan haɗin da dankalin turawa ake haɗashi. Zaku samu dankalin turawa daidai misali wanda za ku iya amfani dashi sai ku ɓare shi ku dafa shi. Sannan ku samu kokomba ku yayyanka shi ku haɗa da wannan dankalin da kuka dafa sai ku markaɗa su. Sai ku samu madarar shanu. Yawancin madarar shanu ana samun ta a wajen fulani, ba nono ba madarar ake buƙata. Idan kun zuba madarar shanu sai ku haɗa da zuma ku juya wannan haɗin sosai ku shanye.


Wannan haɗin zaki yi shine daidai cikin ki ma'ana daidai yadda zaki iya shanyewa a wannan lokacin. Amma idan kina da wajen da zaki iya ajiye shi ba tare da ya lalace ba to zaki iya yi da yawa ki ajiye shi kullum ki ringa sha.


Kuma shi wannan haɗin zaki tsawon wata kin sha a kullum. Kada kice zaki kwana 2 ko sati 1 ko sati 2 kice zakiga wani sauyi.  Idan kinaso kiga yaimiki aiki kuma kin samu abinda kikeso to zaki tsawon kwanaki 30 zuwa 40 domin yai miki aiki sosai. Indai ƙarin girman mazaunai ne wannan haɗin zai taimaka miki wajen ƙara girman sa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post