Nafisa Ishaq Ta Nemi Afuwar Malam Aminu Daurawa Akan Cin Mutuncin Da Ta Yi Masa
Nafisa Ishaq Ta Nemi Afuwar Malam Aminu Daurawa Akan Cin Mutuncin Da Ta Yi Masa |
Jaruma a masana'antar Kannywood Nafisa Ishaq ta nemi afuwar shehin Malami Aminu Ibrahim Daurawa kan ya yafe mata akan kalaman ta da ta yi wanda ta zage shi a cikin wani faifan bidiyo da ta fitar a shafin ta na TikTok inda ta ci mutuncin malamin tare da faɗar maganganun masu nauyi akan sa.
Hakan dai ya faru ne biyo bayan wasu Kalamai da malamin yai a cikin karatun sa da yai a wani faifan bidiyo da yai ta yawo a kwanakin baya, inda a bidiyon aka jiyo malamin yana faɗin cewa al'aurar mace shine guri mafi muni a jikin ta inda malamin yace waje ne mafi muni tunda ta wajen ne duk wata najasa da Ƙazanta ke fita.
Hakan ne ya jawo cece-kuce inda al'umma da dama kowa ke faɗin albarkacin bakinsa wasu na ganin cewa bai kamata malamin yai wannan kalaman ba, sai dai ana ganin cewa ba'a yiwa furucin malamin kyakkyawar fahimta ba sai dai wasu matan sun yi Allah wadai da furucin malamin inda suka dinga mayar masa da martani.
A cikin waɗanda suke sukar malamin game da wannan kalaman har da Nafisa Ishaq wacce tafi sauran matan zaƙewa inda ta fitar da wani bidiyo tana maida martani ga malamin har da zagin sa hakan dai ya jawo cece-kuce a tsakanin al'umma wanda ake ganin rashin tarbiyyar ta. Inda har wasu ke yin barazana ga rayuwar ta cewa za su kashe ta.
Ganin barazanar da ake yi ga rayuwar ta ne yasa ta fito tana neman afuwar malamin inda ta yi wani bidiyo ta nuna nadamar ta bisa abinda ta yi, tace ina neman afuwar malam don Allah ka yafe min nasaba na yi kuskure. Daga baya kuma ta sake fitar da wani bidiyo inda ta ƙara fitowa tana neman malMasaamin ya yafe mata.
A jiya na yi magana ta sautin murya inda na bada haƙuri, amma naga hakan bai wadatar ba shine yasa a yau na sake yin wani faifan bidiyo domin na ƙara baiwa Malam haƙuri da sauran al'ummar musulmi akan su yafe min, a cewar Nafisa. Sai dai wasu na ganin cewa bai kamata a rabu da ita ba ya dace a yi mata hukunci sannan sai kuma ai mata afuwa domin hakan ya zama darasi ga sauran mata masu irin halin ta.
Leave Comments
Post a Comment