Muhimmin abu game da raƙumi — Android Pols - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Muhimmin abu game da raƙumi — Android Pols

Muhimmin abu game da raƙumi

Muhimmin abu game da raƙumi 


Raƙumi yana iya sha ruwan ɗanɗano da na gishiri. Hatta ruwan Tekun da ake kira da "Dead Sea" yana iya shan ruwa ba tare da komai ya same shi ba. 


Wannan ya samo asali ne sakamakon Allah Ya yi masa wadansu sassa dake tace ruwa, suna raba gishiri a cikinsa suna mayar da shi ruwan sha mai tsafta. 


Raƙumi kuma yana cin ƙayoyi, amma ba sa cutar da cikinsa ko hanjinsa saboda yawun Raƙumi yana narkar da ƙayoyi nan take, kamar sinadarin acid.


Raƙumi yana da wani ƙyalle a idanunsa: ɗaya yana siranta kuma kamar 'glass' yake; ɗayan kuma yana kauri da tsoka. Idan iska mai ƙura ta taso a wurin hamada, Raƙumi yana rufe ƙyallen ido mai gilashin don kada ƙura ta shiga idanunsa. 


Haka kuma, Raƙumi yana iya canza zafin jikin sa: idan yana wurin da akwai yanayin sanyi, sai zafin jikinsa ya ƙaru; idan kuma akwai zafi, misali wurin da ake da hamada, sai zafin jikinsa ya ragu.


Haƙiƙa Allah Ya yi gaskiya da Ya tambaye mu shin, ba za mu yi duba i-zuwa yadda Ya halicci Raƙumi ba? أَفَلَا يَنْظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel