Mijina Baya kwana A Ɗakina Tun Bayan Da Abokiyar Zamana Ta Tafi Yin Wankan Jego Gidan Su - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Mijina Baya kwana A Ɗakina Tun Bayan Da Abokiyar Zamana Ta Tafi Yin Wankan Jego Gidan Su

Mijina Baya kwana A Ɗakina Tun Bayan Da Abokiyar Zamana Ta Tafi Yin Wankan Jego Gidan Su
Mijina Baya kwana A Ɗakina Tun Bayan Da Abokiyar Zamana Ta Tafi Yin Wankan Jego Gidan Su 

 


Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin na tambayoyin ku wanda muke miƙawa malamai su kuma su amsa. A yau wata tambaya ce da aka daɗe ana yin ta wanda yau muka zo muku da amsar. Da fatan Allah yasa mu amfanar daga cikin abubuwan da zamuji.


A lokuta da dama mata sune suke yawan yin tambayoyi akan abubuwan da suka shige musu duhu, musamman al'amuran da suka shafi zamantakewar su ta aure, suna yawan turo da tambayoyi akan neman mafita ga abubuwan da suka shige musu duhu ko neman ƙarin bayani. Ko kuma su ta wasiƙa akan neman sharhi ko makamancin haka.


Kamar yadda na faɗa tun a farko cewa ita wannan tambayar ana yawan yin ta, amma wannan lokacin dai gashi mun samu kawo muku amsar wannan tamabar. Tambayar kuwa ita ce kamar haka.


Malam barka da wannan lokacin da fatan kana lafiya Allah yasa haka amin. Dan Allah ina so a amsa min wannan tambayar, mijina ne kuma mu biyu ne a wajen shi sai abokiyar zama na ta haihu wanda yasa ta tafi gidan su yin wankan jego, to wallahi malam tun lokacin da tafi gida yin wankan bai ƙara shiga ɗakina ba da niyyar yin mu'amalar aure ba.


Idan ya shigo ɗakina to wani abin zai ɗauka ya fita, wannne ne kawai yake saka shi shiga ɗakina, amma ba domin yin mu'amalar aure ba.  Amma kuma abin mamaki jiya tana dawowa daga wankan jegon sai gashi ya shiga ɗakin ta ya kwana tare da ita. Ni kuwa tun bayan da ta tafi bai kuma kwana tare dani ba. Shine abun ya dameni, malam mene matsayi na.


Ga amsar da Malam ya bayar kamar haka. To da farko dai ki fara tambayar sa ko hakan yana da asali a cikin addini ko kuma dai al'ada ne, domin akwai waɗanda suke yin amfani da al'ada wanda idan ta tafi wankan jego gidan su bayan kuma ga wata matar amma wai ba zai shiga ɗakin ta ba tunda ɗayar ba ta gidan. Kuma shi a tunanin sa yin hakan wai adalci yai.


Kinga hakan kenan yana nuna jahilci da rashin ilimi, domin auren mata biyun bai yi masa amfani ba. Domin idan yana da ilimin addini da bai aikata hakan ba, amfanin auren mata biyu idan ɗaya daga cikin su batada lafiya ko kuma idan ta haihu to sai ka koma wajen ɗayar, ko kuma idan ɗaya daga ciki tana rashin lafiya ko makamancin haka. 


Don haka wannan abin da yai ba daidai bane kuma ki sanar dashi cewa ya yi kuskure, ki same shi cikin hikima kiyi masa bayanin cewa ya yi kuskure, idan kuma bai ɗauka ba sai ki samu wani na kusa dashi wanda yake jin maganar sa sai ki faɗa masa shi sai ya same shi yai masa magana ya fahimtar dashi.


Domin gaskiya abinda yai zalunce ne kuma ya danne miki haƙƙin ki, a addini idan mutum yana da mace guda biyu ko sama da haka idan ɗaya daga ciki tayi tafiya idan ta dawo ba'a rama mata kwanakin da ta yi, amma idan mijin ne yai tafiya ya dawo wannan tilas ne a sake yin rabon kwana, sai dai idan ya yi tafiyar ne da bashin kwanan wata akan sa wannan dole ne idan ya dawo sai ya rama mata.


A ƙarshe Malam yayi kira ga jama'a da su dinga neman ilimin addini da ilimin sanin zaman aure, domin rashin sanin ilimin rayuwar zaman aure yana ɗaya daga cikin abubuwan da kae jawo matsalar rashin fahimta tsakanin ma'auratan. Domin shi wannan mutum idan da yasan ilimin sanin zaman aure da bai yi miki wannan abin ba.


Daga ƙarshe Malam ya ja hankalin ma'aurata da su kula sosai kuma su tashi su nemi ilimi. Da fatan Allah yasa wannan saƙon ya isa ga dukkan ma'aurata wanda suke da aure da kuma wanda suke shirin yi anan gaba.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel