Menene Vernix Caseosa, farin abu dake bayyana a jikin jarirai idan an haife su

Menene Vernix Caseosa, farin abu dake bayyana a jikin jarirai idan an haife su
Menene Vernix Caseosa, farin abu dake bayyana a jikin jarirai idan an haife su


Vernix Caseosa wani farin abune mai danqo da maiqo da ake haifar jarirai dashi a fatar jikinsu.


Yana bawa fatar jariri kariya daga abubuwa kamar :- 


 -Hana shigar ruwan mahaifa (Amniotic fluid) cikin fatar jikin jariri.


-Bayar da kariya daga qwayoyin cututtukan da suka shiga jikin mahaifiyar jariri (ascending infections).


-Da sauran su 


Bayan an haifi jariri,barin vernix caseosa a jikinsa bashi da illa, ba kuma qazanta bane kamar yadda ake fada. 


Qaranchi ko yawan  vernix caseosa a fatar jariri nada alaqa da yawan watannin jariri a ciki. Jarirai da aka haifa basu kai wata tara ba sunfi zuwa da vernix mai yawa saboda fatar su bata fara tsotse shi ba (absorption).


Jariran kuma da suka kai wata tara ko sama da haka, vernix din jikinsu baya kaiwa yawan na jariran da basu kai wannan lokacin a ciki, saboda fatar jikinsu tayi absorbing vernix din.


Vernix caseosa na taimakawa jikin jariri a awannin farko bayan haihuwa wurin samar da dumi da zafin jiki da hana jariri saurin bushewar fata.


Rashin yiwa jariri wanka a awannin farko ko kuma bayan awa ashirin da hudu ba laifi bane face taimakawa lafiyar jariri, amma sanin muhimmancin al'ada da mutunta tsarin rayuwar mutane yasa ba'a hana yiwa jarirai wanka ranar da aka haifesu indai masu lafiya ne.


Vernix Caseosa ba qazanta bane!


Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad 

RN,RM,PND


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post