Menene matsayin haɗin lemo da madara ga jikin ɗan adam? |
Ana mun tambaya sosai akan shin da gaske shan hadin Lemo da Madara ga macen data haihu yana ƙarin jini?
Gaskiya amsar ba haka take ba domin Kalar nau'in lemon (Malt)yana qunshe da sinadaran carbohydrate da suke samar da kuzari (energy) da sauran sinadarai irin su vitamin da mineral.
Ita kuma madara tana dauke da sinadarin protien wanda yake taimakawa wurin samarwa da gyara hallitar tissue da wasu daga cikin dangin vitamin da mineral.
Nasan wasu zasuce to Idan hakane me yasa ake cewa a siya a kawowa mace idan ta haihu?
Naƙuda abune da yake qarar da kuzarin mace da saka galabaita, zaka samu mace tazo asibiti haihuwa amma wata qila rabonta da cin abinchi anfi awa ashirin da hudu, ba kowa bane ciwo ke bashi damar cin abinci ba.
Wani lokacin kuma kana kallon wata macen kasan ba ta samun abinchi mai gina jiki gaba daya (malnourished) dole a tallaafa mata, wasu matan idan ba wannan hadin na Lemon da Madarar da akace a siyo mata ba, ba zata samu damar cin wani abu mai dadi ba har bayan sallamar ta daga gadon asibiti.
Hadin Lemo da Madara na daga cikin hanyoyi mafi sauqi na kawar da yunwa.
Kuma ma dai ba kowa ake cewa ya sayi Lemo da Madara ba domin wasu basa buqatar sa. Saboda haka Idan ance asaya a daina qorafi don Allah.
Allah ya horewa mazaje da iyaye maza sararin kula da iyali. Ameen!
Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad
RN,RM,PND