Menene ke kawo ciwon nono da maganin ciwon nono — Android Pols
![]() |
Menene ke kawo ciwon nono da maganin ciwon nono |
Aslm dan allah doctor ni budurwace nake fama da ciwan nono. Yanzu shekarata 20 tin farkon halittar fitowar mama ajikina yakemun ciwo kana nonon in akabugeni atsakiyar bayana nakejin zafin.
Ciwon nono ga 'yan-mata masu kananan shekaru yawanci baya nuna cewa sunada wata babbar matsala a nonon su. Yakan zamo yana da alaƙa ne da canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikinsu (hormonal imbalances). Wadannan sinadaran suna shafar balaga, jinin haila, ko girman nonon mace.
Yawancin mata matasa suna jin zafin nono ko rashin jin daɗi a matsayin wani ɓangare na tsarin girman halittar jikinsu. Ana kiransa da ciwon nono na lokaci-lokaci (cyclical breast pain), kuma yawanci yana warkar da kansa bayan wani lokaci, ko kuma mace taji sauƙinsa bayan ta sami sauyin rayuwa idan tayi aure.
Amma, idan ciwon nonon ya zamo mai tsanani kuma bai daina ba na tsawon lokaci, ko ya hadu da kumburi ko wasu canje-canje marasa kyau a nono, ko nono guda daya ya shafa na tsawon lokaci, ko ba yana faruwa bane a lokacin jinin al'ada, to, ya kamata kije asibiti domin likita ya dubaki ido-da-ido.
Sa'annan ya kamata ki san cewa ciwon nono a daidai shekarunki na yanzu, zai iya zamowa sakamakon abubuwa ne kamar haka:
1. Sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikinki (hormonal changes), kuma shine ake kira "cyclical mastalgia". Wannan ba matsala bane In-sha-Allah.
2. Budewar fatar kirjinki, da kuma habakar girman tsokar nononki (developmental stretching of skin and tissues as the breasts grow).
3. Tasiranruwar fata da tsokar nononki idan aka taba su (breast sensitivity), domin wasu matan ko an taba nononsu basu jin komai, amma wasu ko yaya aka taba su, to , suna tasiranruwa sosai. Wannan yanayin halitta ne.
4. Rashin samun halittar kasusuwan baya, kirji, da kafadu masu kyau (poor posture). Wannan yana nufin idan halittar kasusuwan kirjinki, da kafadunki, da bayanki sun sunkuya basu tsaya a tsaye kyam ba, to hakan zai sanya tsokoki da fatar nononki su takure, daga nan sai nononki ya rika yi miki ciwo akai-akai, har zuwa bayanki. Idan haka halittar kasusuwan kirjinki suke, to, zaki iya samun saukin ciwon ne ta hanyar yawan yin atisayen bankare kirjinki da bayanki (postural exercises), tareda zama ko kwanciya a wuraren da bayanki da kafadunki ba zasu takura ba.
5. Canje-canjen nono sakamakon kullutun nono (fibrocystic breast changes), wanda yake faruwa saboda kullum fibroadenoma. Fibroadenoma shine kullutun nono wanda yake sanya tsayuwar nono kyam. Wani lokacin yakan kumbura ko ya gundi ruwa, ya haddasa jin zafin nono idan aka taba ko ba'a taba ba.
WalLahu A'lam.
USMAN SHEHU HASSAN
Leave Comments
Post a Comment